Sabon Tarihi: An Bayyana yadda Kwastam Ke Tattarawa Gwamnati N20bn a Kowace Rana

Sabon Tarihi: An Bayyana yadda Kwastam Ke Tattarawa Gwamnati N20bn a Kowace Rana

  • ACG Babatunde Olomu, shugaban kwastam na tashar Apapa, ya jagoranci tattara wa gwamnati Naira tiriliyan 3.7 a watanni 16
  • Shugaba Bola Tinubu da Kwastam, sun sanar da cewa Najeriya da Kwastam sun zarce burinsu na samun kudaden shiga a 2025
  • A wannan rahoto, an yi bayani dalla dalla kan yadda Kwastam ta rika tatso fiye da Naira biliyan 200,000 a kowanne wata a Apapa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – A cikin watanni 16 kacal, hukumar kwastam ta tattaro wa gwamnatin tarayya sama da Naira tiriliyan 3.7 tare da kwace haramtattun kaya masu yawa.

Hukumar ta tatso kudaden ne a tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya, watau Apapa da ke Legas, karkashin jagorancin ACG Babatunde Olomu.

Hukumar kwastam ta dawo tara wa gwamnati Naira biliyan 21 a kowace rana a tashar Apapa.
Shugaban kwastam na tashar Apapa, ACG Babatunde Olomu ya mika shugabanci ga Emmanuel Oshoba. Hoto: @CustomsNG
Source: Twitter

Najeriya ta cimma burinta na kudaden shiga

Wannan nasara da ACG Olomu ya samu, ta kara tabbatar da kwastam a matsayin ginshikin tattalin arzikin Najeriya da kuma kare tsaron kasa, inji rahoton Business Day.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta cimma burinta na samun kudaden shiga na shekarar 2025 kafin shekarar ta kare.

A cewar shugaban kasar, wannan nasara da aka samu zai rage dogaron Najeriya da karbo bashin waje wajen aiwatar da kasafin kudi.

Shugaba Bola Tinubu ya shaida haka ne yayin da yake karɓar bakuncin wasu masu ruwa da tsaki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kwastam ta zarce hasashen kudaden shiga

A ranar da Tinubu ya yi wannan sanarwa, ita ma hukumar kwastam ta sanar da cewa ta zarce hasashen kudin shigarta na rabin shekarar 2025 da 11.85%.

Mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Maiwada, ya ce hukumar ta tara Naira tiriliyan 3.68 daga Janairu zuwa Yuni, 2025, wanda ya kai 55.93% na burinta na shekarar.

Abdullahi Maiwada ya bayyana cewa wannan kudin da hukumar ta tattara na haraji ya zarce hasashen kudin shigarta da Naira biliyan 390.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai yi jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya

Kudaden da kwastam ta tatso a Apapa

Jaridar Tribune ta ce nasarar Kwastam ba za ta iya cika ba, ba tare da gudummawar sashen rundunar na tashar Apapa ba, wanda shi ne sashen kwastam mafi girma a kasar.

ACG Olomu ya hau kujerar shugabancin sashen ne a ranar 5 ga Mayu, 2024. Tun daga lokacin ya samar da jimillar Naira tiriliyan 3.7 zuwa watan Yuli, 2025.

An ce Kwastam ta tattarowa gwamnati Naira tiriliyan 3.7 a cikin watanni 16 a tashar Apapa, Legas.
Wasu ma'aikata na tafiya a babbar tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas. Hoto: World Bank
Source: UGC

Kudin da kwastam ta samu a 2024

  • Mayu 2024 – Naira biliyan 175.1
  • Yuni 2024 – Naira biliyan 178.2
  • Yuli 2024 – Naira biliyan 201.8
  • Agusta 2024 – Naira biliyan 189.5
  • Satumba 2024 – Naira biliyan 193.9
  • Oktoba 2024 – Naira biliyan 264.4
  • Nuwamba 2024 – Naira biliyan 229.3
  • Disamba 2024 – Naira biliyan 252.5

Kudin da kwastam ta tara a 2025

  • Janairu – Naira biliyan 269.3
  • Fabrairu – Naira biliyan 216.9
  • Maris – Naira biliyan 215.9
  • Afrilu – Naira biliyan 230.7
  • Mayu – Naira biliyan 230.7
  • Yuni – Naira biliyan 209.1
  • Yuli – Naira biliyan 214.5

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da 'yar takarar PDP a kotu kan zargin sabawa doka

Jimillar da aka samu a cikin watanni 16 ta kai Naira tiriliyan 3.709.

FIRS, Kwastam sun tatso Naira tiriliyan 21

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumomin Najeriya biyar, sun tattarowa gwamnati Naira tiriliyan 21.22 a cikin watanni shida na farkon 2025.

Hukumar FIRS ta fi kowace hukuma tara haraji, inda ta samu N13.76tn, sai NUPRC da ta samu N5.21tn, sannan Kwastam ta tara N2.02tn daga kuɗin shigo da kaya.

Jimillar kuɗaɗen da aka tara ya kai kashi 58% na hasashen kasafin kuɗi na 2025, alamu na cewa gwamnati za ta iya zarce burinta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com