Hukumar Kwastam: Mutane kusan 600,000 Sun Nemi Guraben Aiki da ba Su kai 4,000 ba

Hukumar Kwastam: Mutane kusan 600,000 Sun Nemi Guraben Aiki da ba Su kai 4,000 ba

  • Hukumar Kwastam takasa ta bayyana cewa an tantance sunaye 'yan Najeriya 286,697 daga cikin masu neman aiki 573,523
  • Ta bayyana cewa wadannan mutane su su ka tsallake zuwa zagaye na biyu na neman guraben aikin da ta tallata tun a 2024
  • Hukumar ta ce a zagaye na biyun, za a gudanar da jarrabawa ta kwamfuta domin kare tantance su, sai a zabi mutane 3,927 a cikinsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaHukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa ta karɓi takardun masu neman aiki akalla 573,523.

Ta karbi wannan adadi ne daga masu neman aiki a matakin farko na shirin daukar sababbin ma’aikata da aka fara tun ranar 27 ga Disamba, 2024, da aka tallata a jaridu.

Kara karanta wannan

Sabon tarihi: An bayyana yadda Kwastam ke tattarawa gwamnati N20bn a kowace rana

Sama da mutum 500,000 sun nemi aikin Kwastam
Wasu daga cikin jami'an hukumar kwastam ta kasa Hoto: @CustomsNG
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Maiwada, ya fitar a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar kwastam na shirin daukar ma'aikata

Vanguard ta ruwaito cewa Abdullahi Maiwada ya bayyana cewa bayan tantance takardu, an fitar da jerin sunayen mutum 286,697 da za su ci gaba zuwa mataki na gaba.

Ya ce za a kara tantance wannan adadi ne domin cike guraben aiki 3,927 da suka shafi matakan Sufritanda da wasu mukamai biyu.

An fara tantance masu neman aikin Kwastam
Wasu daga cikin jami'an hukumar Kwastam Hoto: @CustomsNG
Source: UGC

Ya ce:

“Wannan mataki wani bangare ne na kokarin hukumar wajen karfafa yawan kwararrun ma’aikata da inganta ayyuka."

Jami’in hulɗa da jama’ar ya bayyana cewa za a gudanar da ita ta yanar gizo, wato mataki na biyu na daukar aikin daga ranar 14 zuwa 21 ga Satumba, 2025.

Hukumar kwastam ta shawarci masu neman aiki

Ya ce wannan tsarin yana nuna sadaukarwar hukumar wajen samar da gaskiya, sauƙin shiga da adalci ga duk masu neman guraben aiki.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da 'yar takarar PDP a kotu kan zargin sabawa doka

Sai dai ya jaddada cewa jarabawar ba ta dace da wayar hannu ba, kuma akwai buƙatar a yi amfani da kwamfuta mai kamara.

Maiwada ya ce:

“Zai zama dole a tantance fuskar mutum kafin fara jarabawa, don haka ana bukatar ‘masu neman aikin su kasance cikin tsabta da nutsuwa domin kauce wa matsala.z"

Ya gargadi su da su guji motsi da hayaniya ko yawo yayin jarabawa, domin tsarin zai iya fitar da su daga shafin kai tsaye idan ya gano hakan.

Maiwada ya kara da cewa akwai shirin gwaji da za a gudanar kwanaki biyu kafin jarabawar don koya wa masu neman guraben aiki yadda tsarin ke aiki.

Jami'an kwastam sun yi kame

A baya, mun wallafa cewa hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Seme, ta sanar da damke wata mota makare da ke dauke da sinadarin mercury da aka shigo da su kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargi ana amfani da shi wajen hada bam, kuma an kama su a wani samame da jami’anta suka gudanar yayin sintiri a hanyar Legas zuwa Badagry.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Kungiyar dattawan Arewa ta samo.mafita ga gwamninin yankin

Shugaban hukumar Kwastam a Seme, Kwanturola Ben Oramalugu, ya tabbatar da cewa an kama mutum guda da ake zargi da mallakar motar da haramtattun kayan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng