Najeriya Ta Yi Gargadi bayan Luguden Wutan Isra'ila a Qatar da Jiragen Yaki
- Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwa kan harin jiragen saman Isra’ila da aka kai a kasar Qatar wanda ya kai ga shugabannin Hamas
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce lamarin na barazana ga zaman lafiyar yankin da kuma kokarin diflomasiyyar da ake yi
- Najeriya ta yi kira ga dukkan bangarori da su yi hattara, su guji tashin hankali, tare da komawa teburin sulhu domin warware rikicin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa kan rahotannin da suka nuna cewa Isra’ila ta kai hari da jiragen sama a birnin Doha na Qatar.
Sanarwar ta nuna cewa wannan lamari na iya shafar zaman lafiyar yankin, tare da kawo tarnaki ga kokarin diflomasiyya na magance rikicin Isra’ila da Falasdinawa.

Source: Twitter
A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a X, gwamnati ta ce dole ne a mutunta kowace kasa da kuma bin ka’idojin dokokin kasa da kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran Najeriya na zaman lafiya
Gwamnati ta yaba da rawar da Qatar ke takawa a matsayin mai shiga tsakani a yankin, inda ta sha gudanar da tattaunawa da sulhu tsakanin bangarorin da ke gaba da juna.
Ta kara da cewa Najeriya na kira ga dukkan bangarori da su yi hattara, su guji kara tsananta rikici, tare da jajircewa wajen komawa tattaunawa domin samun zaman lafiya mai dorewa.
An kuma mika sakon jaje ga wadanda abin ya shafa tare da jaddada goyon bayan Najeriya ga duk wani shiri da zai rage tashin hankali da inganta tattaunawa.
Matsayar Najeriya kan diflomasiyya
Ma’aikatar harkokin wajen ta ce Najeriya za ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya ta hanyar Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa.
Punch ta ce za a yi haka ne domin ganin an tabbatar da zaman lafiya, tsaro da bin doka a Gabas ta Tsakiya da sauran sassan duniya.

Source: Facebook
Rahotannin ma’aikatar lafiya ta Falasdinawa a Gaza sun ce fiye da mutane 62,000 ne suka rasa rayukansu tun bayan fara hare haren Isra'ila a Gaza a kusan shekara biyu da suka gabata.
Rawar da Qatar ke takawa a yankin
Qatar ta kasance cibiyar siyasa ga shugabannin Hamas tsawon shekaru, inda take taka muhimmiyar rawa a tattaunawar sulhu tsakanin bangarori.
Lamarin da ya faru a Doha ya tayar da damuwa kan tasirin Qatar a matsayin mai shiga tsakani, yayin da kasashe ke ci gaba da neman hanyoyin da za su kawo karshen tashin hankali a yankin.
An kashe mai goyon bayan Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun harbe wani matashi mai goyon bayan Isra'ila a kasar Amurka.
Rahotanni sun bayyana cewa an harbe Charlie Kirk ne yayin wani taro a wata jami'a yana tsaka da yin bayani.
Shugaban Amurka, Donald Trump da Benjamin Netanyahu na Isra'ila sun nuna damuwa sosai kan kashe matashin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

