'Yan Sandan Kano Sun Yi Bayani kan Zargin Garƙame Ɗan Jarida na Tsawon Awanni

'Yan Sandan Kano Sun Yi Bayani kan Zargin Garƙame Ɗan Jarida na Tsawon Awanni

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta yi karin bayani a kan rahoton cewa ta tsare wani dan jarida a jihar mai suna AbdulAziz Aliyu
  • Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya yi karin haske bayan an zargi 'yan sanda da tsare dan jarida kan wani labari
  • Kiyawa ya bayyana cewa ba su rike AbdulAziz ba, amma an gayyace shi domin yin karin bayani kan labarinsu da aka kai korafi a kai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar da sanarwa tana musanta rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an tsare wani dan jarida mai suna Abdulaziz Aliyu.

Wannan na zuwa a matsayin martanin cewa rundunar ta tsare AbdulAzizi a ofishin ‘yan sanda na Court Road da ke Gyadi-Gyadi, bisa wani rahoto da ya wallafa.

Kara karanta wannan

'Sun fara kamfe a sakaye,' INEC ta fadi yadda 'yan siyasa su ke birkita mata lissafin 2027

Yan sandan Kano sun magantu kan tsare dan jarida
Hoton Kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, da wasu jami'ai Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Rundunar ta yi bayani ne a cikin sanarwar da magana da yawunta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun musanta tsare dan jarida

Daily Trust ta wallafa cewa sanarwar da Kiyawa ya fitar a Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, rundunar ta ce ba a tsare dan jaridar ba.

Ta ce abin da ya faru shi ne rundunar ta gayyace shi bisa wani korafi da aka shigar a kansa domin gudanar da bincike.

Sanarwar ta kara da cewa an saki Abdulaziz Aliyu bayan ya bayyana a gaban ‘yan sanda, kuma an ba shi beli tare da umarnin ya dawo ranar 10 ga Satumba, 2025.

Yan sandan Kano sun ce bincike su ke yi
Hoton Kakakin rundunar yan sandan Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kiyawa ta cikin sanarwar ya bayyana cewa an umarce shi da ya dawo ofishinsu domin a dora da bincike da tambayoyi a kan batun.

Ya ce bayan binciken da rundunar ta gudanar tare da shugabannin Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Kano, an gano cewa Abdulaziz Aliyu ba, da Yakubu Salisu – wanda ya fitar da rahoton ba su da rajista da NUJ.

Kara karanta wannan

'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina

Alakar 'Yan sandan Kano da 'yan jarida

Rundunar ta bayyana cewa tana da alaka mai kyau da ‘yan jarida da kafafen yada labarai a fadin jihar, kuma tana mutunta ka’idojin ‘yancin fadin albarkacin baki.

Ta kara da cewa 'yan sandan suna mutunta ‘yancin kafafen yada labarai kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Sai dai kuma rundunar ta bayyana cewa rahoton da Yakubu Salisu ya fitar wani yunkuri ne na bata suna da tunzura jama’a da lalata dangantaka mai kyau tsakanin ‘yan sanda da kafafen yada labarai.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa za a gudanar da bincike a cikin gaskiya da kwarewar aiki.

Haka kuma, rundunar ta yi kira ga jama’a da su rika tantance bayanai kafin yadawa, tare da ba ‘yan sanda goyon baya a kokarin su na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kano: Gwamna Abba ya tuno gwawarmayarsa

A baya, kun ji cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa ya fuskanci ƙalubale da matsaloli iri-iri tun bayan nasarar da ya samu a zaɓen 2023 a jihar.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke bayan tono gawar malamin Musulunci a kabari aka kona ta

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, inda ya bayyana irin gwagwarmayar da suka fuskanta.

Ya bayyana cewa amma wannan gwagwarmaya ta kara masa kwarin gwiwa wajen kara daukar alkawarin da ya yi wa mutanen Kano da muhimmanci kafin 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng