EFCC Ta Gurfanar da 'Yar Takarar PDP a Kotu kan Zargin Sabawa Doka

EFCC Ta Gurfanar da 'Yar Takarar PDP a Kotu kan Zargin Sabawa Doka

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da ‘yar takarar majalisar wakilai ta PDP a gaban kotu a Abuja bisa zargin karbar kudi sama da abin da doka ta amince
  • Esther Ashivilli Dawaki da shugaban kwamitin yakin neman zabenta, Shehu Aliyu Fatange, na fuskantar tuhume-tuhume
  • Alkalin kotun da aka gurfanar da su, ya yi hukunci kan bukatar da lauyoyinsu su ka gabatar a gabansa, ta neman a bada belinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen Kaduna ta gurfanar da ‘yar takarar majalisar wakilai ta PDP a zaben cike gurbi na Chikun/Kajuru, Esther Ashivilli Dawaki.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Esther ne tare da shugaban kwamitin yakin neman zabenta, Shehu Aliyu Fatange, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin badakalar kudi.

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Yadda ta kaya bayan EFCC ta titsiye tsohon shugaban kamfanin NNPCL

EFCC ta kai karar 'yar takarar PDP gaban kotu
Hoton Esther Ashivilli Dawaki da Shehu Aliyu Fatange dauke da allon laifi na EFCC Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cijin wata sanarwa da hukumar EFCC ta sanya a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama wadanda ake tuhuma ne a ranar 16 ga Agusta, 2025, bayan bayanan sirri sun nuna suna da Naira miliyan 26.463,000.00 a cikin wata mota Toyota Corolla 2010, mallakar Shehu Aliyu Fatange da aka ajiye a cikin wani otal a Kaduna.

Wace tuhuma EFCC ke yi wa 'yar takarar PDP?

Ana tuhumar su da laifuffuka guda biyar da suka shafi karbar tsabar kudi sama da abin da doka ta kayyade ba tare da banki ba, wadanda suka kai har Naira miliyan 26.

A cewar EFCC, a ranar 16 ga watan Agusta, 2025, Esther Dawaki ta sa Shehu Aliyu Fatange ya karbi kudi Naira miliyan 26 ba tare da amfani da cibiyar kudi ba, wanda hakan ya sabawa doka.

'Yan PDP sun musanta laifin da ake tuhumarsu

Kara karanta wannan

Mamakon ruwa ya 'daidaita jama'a a Kaduna, sama da mutum 500 sun rasa matsuguni

Esther Ashvilli Dawaki da Shehu Aliyu Fatange sun musanta laifukan da ake tuhumar su da su.

Lauyan masu shigar da kara, M. O. Arumemi ya bukaci kotun ta sanya ranar fara shari'a, tare da neman a tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali.

Yayin da lauyoyin wadanda ake kara, E. N. Ogbu da A. A. Ashat, suka roki kotu ta ba su beli, ko kuma a bar su a hannun EFCC har sai an yanke hukunci kan bukatar belin.

EFCC ta gurfanar da 'yar takarar PDP gaban kotu
Hoton shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, yana jawabi Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Alkali ya tura su gidan gyaran hali

Sai dai alkalin kotun, mai shari’a Emeka Nwite, ya bada umarnin a tura Esther Dawaki zuwa gidan gyaran hali na Suleja, sannan a tura Shehu Aliyu Fatange zuwa gidan gyaran hali na Kuje.

Alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, 2025, domin sauraron bukatar belin.

Mele Kyari ya hadu da EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya kai kansa ga hukumar EFCC.

Kara karanta wannan

"A koresu": Kungiyar 'yan Arewa ta ba Tinubu shawara kan rashin tsaro

Mele Kyari ya je wurin EFCC ne ka.mn wasu tuhume-tuhume da ake yi masa kan yadda ya gudanar da kamfanin a lokacin mulkinsa.

Tuhume-tuhumen na da nasaba da kudin da aka kashe yi wa matatun mai mallakin gwamnati gyara a lokacin da yake rike da kamfanin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng