An Gano Jami’an Tsaro na Taimakawa Yan Bindiga a Bidiyo? Gaskiya Ta Bayyana
- An yi ta yada wani faifan bidiyon jami'an tsaro da ake zargin suna taimakawa yan bindiga a cikin wani daji da aka yi zargin a Najeriya ne
- Wannan ba shi ne karon farko ba da ake yada irin wannan bidiyo wanda ke kara raunana guiwar jami'an sojoji da ke bakin kokarinsu ba
- Binciken kwa-kwaf ya karyata bidiyon da ake yadawa, inda ake ikirarin sojojin Najeriya na ba ’yan bindiga masu yin ta'adi goyon baya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A Najeriya an sha samun wasu rahotanni da ke yada cewa jami'an tsaro na goyon bayan yan bindiga a cikin wani daji.
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta yana cewa sojojin Najeriya na marawa ’yan bindiga baya da aka gano a cikin daji.

Source: Twitter
Binciken kwa-kwaf na Zagazola Makama ya tabbatar da cewa wannan batu ƙarya ne kuma an yi domin rudar da jama'a ne.
Yadda ake yada bidiyon karya kan jami'an tsaro
Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun irin wannan matsala wanda ake yada bidiyo da ke tayar da hankula da saka shakku a yaki da ta'addanci.
Irin wannan bidiyo da ake yadawa na kara jawo tasgaro kan yaki da ta'addanci da ake ta kokarin yi a Najeriya musamman ga jami'an tsaro.
Rundunar 'yan sanda ta musanta rade-radin cewa jirgin sama ya kai kayan abinci ko makamai ga 'yan bindiga a jihar Kogi.
Karin haske daga rundunar 'yan sanda kan lamarin
'Yan sanda sun bayyana cewa jirgin ya shiga aikin yaki da 'yan bindiga ne tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da 'yan banga a Obajana.
Rundunar ta bukaci jama’a da su daina yarda da labaran karya, su rika sauraron bayanai daga hukumomin tsaro tukuna a koyaushe domin gujewa fadawa irin wannan tarko.

Source: Facebook
Bincike ya karyata bidiyon sojoji da 'yan bindiga
Majiyoyi sun gano bidiyon da ake yadawa ya fara bayyana a farkon 2024 daga rikicin Darfur a Sudan kuma ba shi da alaƙa da Najeriya.
Masana sun ce irin waɗannan hotuna na karya suna karya kwarin gwiwar dakarun yaki da ta’addanci, suna kuma ƙara yaɗa tashin hankali a al’umma.
An ja hankalin jama’a su daina yada bidiyoyi marasa tushe saboda hakan na taimakawa ’yan ta’adda da bata kokarin jami’an tsaro.
Binciken ya ce ya kamata a jajirce wajen karyata labaran ƙarya tare da tabbatar da jama’a na samun sahihan bayanai masu inganci.
'Yan bindiga, sojoji sun gwabza fada a Katsina
Kun ji cewa dakarun Operation Fansan Yanma tare da taimakon sauran jami'an tsaro sun fatattaki ‘yan bindiga a karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina.
A yayin da ake musayar wuta, 'yan ta'addan sun kashe shugaban mafarauta, Usman Lawal, sannan su ma an kashe masu mutum daya.

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Harin na yammacin Talata, 9 ga Satumba, 2025, na zuwa ne bayan Gwamna Dikko Radda ya yi magana kan sulhu da 'yan bindiga a Katsina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

