'Dalilin da Ya Sa Aka Sake Fasalin Kabarin Buhari a Daura'
- Wasu hotuna da suka yadu, sun bayyana yadda aka sake fasalin kabarin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura
- Wasu sun ce ya hakan ya dace duba da matsayin da ya rike a rayuwa, wasu kuma na ganin hakan ya saba da koyarwar Musulunci
- Dangin marigayin sun yi bayani kan dalilin da ya sanya aka sake fasalin yadda wurin da kabarin yake a garin Daura dake Katsina
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Daura, jihar Katsina - Sababbin hotuna da bidiyo da suka yadu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda aka sake fasalin kabarin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa na Daura.
Sake fasalin kabarin na marigayi Muhammadu Buhari na zuwa ne makonni bayan an yi jana’izarsa a ranar Talata, 15 ga watan Afrilun 2025.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce ta tuntubi wani dan uwan Buhari, Alhaji Hamisu Haro, wanda ya bayyana dalilin yi wa kabarin kwaskwarima.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro da ƴan bindiga sun gwabza ƙazamin faɗa a Malumfashi, an rasa rayuka
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayi Buhari dai ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan, bayan ya kwanta jinyar rashin lafiya.
Hotunan kabarin Buhari sun yadu
Hotunan gyaran da aka yi wa kabarin sun fito ne lokacin ziyarar da gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai kwanan nan.
A lokacin ziyarar, Gwamna Radda ya roki Allah (SWT) da ya gafartawa marigayi Buhari, ya karɓi kyawawan ayyukansa, ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdaus.
Lamarin ya jawo muhawara a tsakanin al’umma, inda wasu ke ganin cewa matsayin da Buhari ya rike a rayuwa ya cancanci hakan, yayin da wasu ke cewa wannan mataki ya saba da koyarwar addinin Musulunci.
Dangin Buhari sun yi karin bayani
Alhaji Hamisu Haro, wanda ke kula da harkokin gidan tsohon shugaban kasan, ya bayyana cewa katangar da aka yi a wajen kabarin, an yi ta ne kawai saboda tsaro.
Ya ce an yi la’akari da koyarwar addinin Musulunci kafin daukar wannan mataki.
"A wannan lokaci da muke ciki, mun ga dacewar a yi katanga a wajen domin tsaro. Duk wanda zai zo ya yi addu’a zai tsaya daga waje, kamar yadda aka gani a lokacin ziyarar Gwamna Radda."
"Akwai wasu lokuta, wasu mutane saboda kaunar da suke wa marigayin, suka kawo furanni suka ajiye a kabarin, ba tare da saninmu ba. Dole muka cire, domin hakan ya saba da koyarwar Musulunci."
- Alhaji Hamisu Haro

Source: Twitter
Ba a taba kabarin marigayi Buhari ba
Alhaji Hamisu Haro ya kara da cewa, ban da katangar da aka yi, an shimfida siminti kan hanyar zuwa wajen domin hana ambaliyar ruwa da lalata wurin.
Ya tabbatar da cewa kabarin kansa ba a taba shi ba, domin koyarwar addinin Musulunci ta hana hakan.
Yadda Buhari ya yi barazanar tsige minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon man fetur, Dr. Ibe Kachikwu, ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi masa barazanar tsigewa kan tallafin man fetur.
Dr. Ibe Kachikwu ya bayyana cewa Buhari ya tirje sosai kan batun cire tallafin man fetur lokacin da yake rike da madafun ikon kasar nan.
Tsohon ministan ya bayyana cewa Buhari ya fito kai tsaye ya gaya masa cewa zai kore shi idan kokarin da yake na cire tallafin man fetur ya kara jefa 'yan Najeriya a cikin wahala.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

