Tinubu Ya Yi Umarni a Sauke Farashin Abinci domin Talaka Ya Samu Sauki
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga kwamitin majalisar zartarwa ta kasa domin daukar matakai kan farashin abinci
- Umarnin ya mayar da hankali ne wajen tabbatar da tsaro da saukin jigilar kayan gona a manyan hanyoyi domin rage kudin sufuri
- Karamin ministan harkokin noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana haka bayan kammala wani taro a birnin tarayya Abuja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa ga kwamitin majalisar zartarwa ta kasa domin daukar matakan da za su rage tsadar kayan abinci a fadin kasar.
Wannan umarni ya zo ne a daidai lokacin da 'yan kasa ke kara kokawa kan yadda abinci ke lakume kaso mafi tsoka na albashinsu.

Kara karanta wannan
Majalisa na barazanar hada minista da Tinubu kan 'raina' 'yan Najeriya da suka yi hadari

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa karamin ministan noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce shugaban kasa ya nuna damuwa kan yadda matsalolin tsaro da tsadar sufuri ke kara haifar da matsalar abinci a kasar, don haka dole a samar da hanyoyin saukaka jigilar kayan gona.
Umarnin Tinubu a kan sauke farashin abinci
Sanata Abdullahi ya bayyana cewa shugaban kasa ya umarci kwamitin FEC da ya dauki mataki wajen tabbatar da saukin da amincin zirga-zirgar kayayyakin gona a dukkan hanyoyi.
Wannan mataki zai rage kudin daukar kaya da kuma tasirin tsadar sufuri da ya biyo bayan cire tallafin man fetur.
Ya kara da cewa gwamnati ta dauki nauyin tabbatar da cewa kayan abinci suna da saukin samu, araha kuma su kasance suna dauke da sinadarai masu amfani ga lafiyar jama’a.
Shirye-shirye don tallafawa manoma
Vanguard ta wallafa cewa ministan ya ce gwamnatin Tarayya ta tanadi shirin kula da lafiyar kasa domin bunkasa ingancin amfanin gona.
Haka kuma za a gabatar da tsarin karfafa kungiyoyin hadin kai na manoma, domin samar da jarin aiki da karfafa tattalin arzikin kauyuka.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana kallon kungiyoyin hadin gwiwa a matsayin hanyar tattara albarkatu da kirkirar ayyuka, wanda hakan zai inganta rayuwar mutanen karkara.

Source: Twitter
Kalubalen tsadar abinci a Najeriya
Najeriya, wacce tafi kowace kasa a Afirka yawan jama’a, na fuskantar matsanancin matsalar abinci tun bayan cire tallafin man fetur, tsadar sufuri da kuma rashin tsaro a manyan hanyoyi.
Duk da matakan da gwamnati ta dauka, farashin kayan abinci ya ci gaba da zama sama da karfin miliyoyin jama’a.
Duk da haka, shugaba Tinubu a baya ya bayyana cewa Najeriya tana kan hanyar cimma tsayuwa da kafarta ta fuskar abinci.
Za a raba wa manoman Najeriya tallafi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin ba manoma tallafi domin bunksa samar da abinci.
Sai dai gwamnatin ta ce za a dauki sunayen manoma domin tabbatar da cewa tallafin ya isa wajen wadanda suka cancanta.
Rahotanni sun nuna cewa an dauki matakin tantance manoman ne domin cire wadanda za su karbi tallafin ba tare da yin noma ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

