Malamin Addini Ya Faɗi Abin da Zai Faru da Tinubu da Jiga Jigan APC da Za a Watsar

Malamin Addini Ya Faɗi Abin da Zai Faru da Tinubu da Jiga Jigan APC da Za a Watsar

  • Wani babban malami kuma limamin addinin Kirista a Najeriya ya yi hasashen abin da zai faru a zaben shekarar 2027 mai zuwa
  • Fasto Josiah Onuoha ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaben 2027 duk da rikicin da ke cikin jam’iyyar APC
  • Sai dai Onuoha ya bayyana cewa manyan na kusa da Tinubu za a tunɓuke su daga mukamansu, amma za su dawo da ƙarfi nan gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Cocin 'Christ Foundation Miracle International Chapel', Fasto Josiah Onuoha ya yi hasashen zaben 2027 da ke tafe.

Faston ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai ci zaben 2027 duk da rikicin cikin gidan jam'iyyar APC da ke faruwa a wannan lokaci.

Fasto ya yi hasashe kan zaben Tinubu
Fitaccen Fasto Josiah Onuoha da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Josiah Onuoha, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Fasto ya gargadi Tinubu kan zaben 2027

Kara karanta wannan

'Wasu gwamnoni za su sauya sheka zuwa jam'iyyar APC kafin zaben 2027 a Najeriya'

Onuoha ya yi hasashen sauye-sauye kan wasu na kusa da Shugaba Tinubu kafin 2027, inda ya ce mafi kusa da shi za su rasa mukamansu, cewar The Guardian.

Sai dai ya kara da cewa waɗanda aka tumɓuke za su dawo a kan lokacin da ya dace da karfinsu.

Fasto ya ce akwai wadanda suke shirin jawowa Tinubu matsala a zaben 2027 kuma bisa ga dukkan alamu sun fara samun karfi domin cimma burinsu.

An yi hasashe kan zaben 2027 da Tinubu
Shugaban kasa, Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Faston ya ja kunnen Tinubu kan kalubalen 2027

Har ila yau, Fasto ya ce ya samu wahayi daga Ubangiji kan lamarin zaben 2027 da kuma kalubalen da ke cikin zaben inda ya ce ya ba shi amsa kan haka.

Ya ce:

“Da sassafe yau, Ubangiji ya yi magana da ni game da Najeriya da jam’iyya APC, ya ce jam’iyyar za ta shiga rikici wanda zai kifar da manya, kuma shugabannin za su sha wahala.
“Ba zato, mutanen da suka shirya kifar da shugabannin sun fara samun goyon bayan jama’a, daga baya, wadanda aka kifar suka dawo da ƙarfi.
“Wannan lokaci, za su dawo da cikakken iko, su rinjayi abokan gaba, su maida su masu biyayya… sai na ce me yasa? Sai ya ce ya bani amsar 2027.”

Kara karanta wannan

Jerin Lokutan da Shugaba Tinubu ya tafi hutu kasashen waje cikin shekara 2

Onuoha ya caccaki 'yan siyasa kan son zuciya

Limamin cocin ya yi Allah wadai da manufofin son zuciya na wasu ‘yan siyasa, ya kuma bukaci su sauya tunani tare da fifita al’ummar kasa.

Sai dai ya kara da cewa wasu za su dawo da karfinsu bayan tumbuke su domin ci gaba da ba da gudunmawa a gwamnatin.

Fasto ya hango abin da zai faru da Tinubu

A baya, mun ba ku labarin cewa fitaccen fasto, Samuel Ojo, ya ce yunkurin ‘yan adawa na hana Shugaba Bola Tinubu yin tazarce a zaben 2027 ba zai yi nasara ba.

A cewarsa, Ubangiji ya riga da ya rubuta nasarar Tinubu a 2027, don haka, ko ana ha maza ha mata, Tinubu ne mai nasara a zaben .

Ojo ya yi gargaɗi ga 'yan adawa da su hakura da 2027, domin Ubangiji bai gama amfani da Tinubu ba, akwai sauran aiki a gabansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.