Harin 'Yan Boko Haram Ya Fusata Sojoji, Sun Hallaka Tsageru Masu Yawa a Borno

Harin 'Yan Boko Haram Ya Fusata Sojoji, Sun Hallaka Tsageru Masu Yawa a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kara kaimi wajen fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • Sojojin sun kai wasu hare-hare ta sama da kasa bayan wani kazamin hari da 'yan ta'adddan suka kai a karamar hukumar Bama
  • Hare-haren sun yi sanadiyyar tura mayaka da kwamandojin kungiyar ta'addan masu yawa zuwa barzahu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun kai hare-hare ta sama da kasa kan mayakan ISWAP/Boko Haram a jihar Borno.

Sojojin sun kai hare-haren ne a dajin Sambisa da tsaunukan Mandara, inda suka hallaka 'yan ta'adda masu yawa.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno
Hoton kwamandan rundunar Operation Hadin Kai tare da dakarun sojoji Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun farmaki 'yan ta'adda bayan kai hari

Hare-haren sun biyo bayan mummunan harin da ‘yan ta’addan ISWAP su ka kai kauyen Darajamal a karamar hukumar Bama, jihar Borno, a daren ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun badda kama yayin tafka ta'asa a Zamfara

Harin ya jawo asarar rayukan mutane 63, abin da ya sa sojoji suka ɗauki matakin mayar da martani cikin gaggawa.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun farmaki Darajamal, suna harbi ba kakkautawa, inda suka tafka barna kafin su ja da baya zuwa cikin daji.

Wani babban jami’in tsaro, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce jiragen sintiri na ISR sun bi sawun ‘yan ta’addan yayin da suke kokarin janyewa daga kauyen zuwa yankin Arewa cikin rukuni-rukuni.

"Jiragen ISR sun gano motsin ‘yan ta’adda da dama, wasu suna tafiya a layi guda, wasu kuma sun watse zuwa yankin Arewa da sansaninsu."
"Jiragen saman sun yi gaggawar sakar musu bama-bamai masu fashewa. Hare-haren sun yi tasiri sosai, sama da ‘yan ta’adda 30 aka kashe nan take, gawarwakinsu sun tarwatse."

- Wani jami'in tsaro

Jami’in ya kara da cewa, dakarun kasa da aka tura daga sansanonin sojojin da ke kusa, sun shiga wurin jim kaɗan bayan hare-haren don tabbatar da tsaron Darajamal da kuma kwantar da hankalin jama'a.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Katsina, an tura miyagu zuwa barzahu

Sojoji sun yi ruwan wuta a maboyar Boko Haram

A wani ɓangare na ci gaba da farmakin, rundunar sojojin Najeriya ta tura jiragen yaki marasa matuka zuwa tsaunukan Mandara, inda suka kai farmaki kan mafakar ‘yan ta’adda da hanyoyin da su ke bi.

Rahotanni sun nuna cewa jiragen marasa matuka sun kai hare-haren ne a a wurare guda huɗu.

“Hare-haren sun yi matuƙar tasiri. An kashe kwamandoji da dama da mayakansu. An ga sauran suna watsewa cikin daji, suna barin makamai da kuma gawarwakin abokanansu.”

- Wata majiya

Sojoji sun ragargaji 'yan Boko Haram
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mayakan Boko Haram sun birne gawarwarki

Binciken sirri ya nuna cewa tsagin Ali Ngulde na Boko Haram, ya binne gawarwakin mayakansu da suka mutu. An tabbatar da binne akalla gawarwaki 47 a wurare daban-daban.

"An birne gawarwaki 30 a dajin Sambisa, yayin da wasu 17 aka binne su a kananan kaburbura a tsaunukan Mandara."
"An bar wasu gawarwaki da dama a daji domin ‘yan ta’addan ba su da isassun mutane da za su ɗauke su.”

Kara karanta wannan

Shettima ya yi alhini kan kisan Boko Haram, ya ba da tabbacin yin adalci

- Wata majiya

Jami'an sojoji sun hallaka 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a jihar Katsina.

Sojojin sun kashe 'yan ta'adda 23 bayan sun farmakesu a maboyarsu da ke cikin karamar hukumar Kankara.

Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar ceto mutanen da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng