"Ba Ruwan Tinubu," An Jingina Harajin Fetur da Gwamnatin Marigayi Umaru Yar'adua

"Ba Ruwan Tinubu," An Jingina Harajin Fetur da Gwamnatin Marigayi Umaru Yar'adua

  • Shugaban kwamitin gyaran haraji na shugaban kasa ya ce ba gwamnatin Bola Tinubu ta kafa dokar biyan harajin fetur da ake yadawa ba
  • Taiwo Oyedele ya yi karin haske kan harajin wanda 'yan Najeriya za su fara biya kan kowace litar man fetur da suka saya
  • Wannan haraji na 5% ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya bayan bullar labarin cewa za a fara biya a watan Janairu, 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ya ce ba Gwamnatin Tinubu ta kirkiro harajin fetur da ake ta ce-ce-ku-ce a kai ba.

Mista Oyedele ya ce tun shekarar 2007, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Marigayi Umaru Musa 'Yar'adua ta kirkiro harajin 5% kan kowace litar fetur.

Shugaban kwamitin haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele.
Hoton shugaban kwamitin sauya fasalin haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele Hoto: Taiwo Oyedele
Source: Twitter

Mista Oyedele ya yi wannan bayani ne a cikin shirin The Morning Brief na Channels Television a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kungiyar TUC ta ja daga, ta ba gwamnatin Tinubu kwanaki 14 ta janye harajin fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka kafa dokar harajin fetur a Najeriya?

Ya ce an kafa wannan doka tun a shekarar 2007, amma ba a taba aiwatar da ita ba saboda gwamnatin wancan lokacin na bayar da tallafin mai.

“Abu mafi muhimmanci da mutane ya kamata su sani shi ne wannan doka ba gwamnatin nan ta kawo ta ba. Tun a 2007 aka kafa ta,” in ji shi.

A ‘yan kwanakin nan, labarin cewa yan Najeriya za su fara biyan karin kashi 5% a matsayin haraji, kimanin N45 kan kowace lita ta man fetur ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasa.

Wasu sun yi zargin cewa za a fara aiwatar da shi daga watan Janairu, lamarin da ya haddasa fushi da adawa daga kungiyoyin kwadago da na farar hula.

Shin gwamnatin Tinubu ta kirkiro harajin?

Sai dai Oyedele ya ce wannan kudin ba ya cikin sababbin dokokin haraji da shugaban kasa ya rattaba musu hannu a bana.

Kara karanta wannan

Tinubu ya waiwayi daliban da aka sace lokacin Jonathan, ya ba su tallafin N1.85bn

A cewarsa, lokacin da ake aikin gyaran dokokin haraji, an dauko batun amma sai aka gamo cewa akwai dokar da ta tanadi wannan haraji a karkashin dokokin Hukumar Kula da Hanyoyi ta Tarayya (FERMA).

Ya bayyana cewa bisa ga tsarin dokar, 40% na kudin zai tafi ga hanyoyin tarayya, yayin da 60% kuma zai shiga asusun jihohi, rahoton Daily Post

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton mai girma shugaban Najeriya,Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Amfanin da za a yi da kudin harajin fetur

Ya kara da cewa babu wani tabbaci cewa za a fara karbar kudin daga watan Janairu, 2025 sabanin jita-jitar da ake yadawa.

Tun bayan bullar labarin, Kungiyar Kwadago ta TUC ta yi barazanar tsunduma yajin aiki, yayin da kungiyoyin masu zaman kansu suka yi adawa da karin kudin.

Amma Oyedele ya dage cewa idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata, zai taimaka wajen gyara da kula da hanyoyin mota a kasar, lamarin da dukkannin ‘yan kasa za su amfana da shi.

TUC ta ba gwamnatin Tinubu wa'adi

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ƙwadago (TUC) ta yi fatali da shirin gwamnatin tarayya na ƙara harajin 5% a kan man fetur.

Kara karanta wannan

Jerin jihohin da mafi karancin albashi ya kusa N100,000 ko sama da haka a Najeriya

TUC ta bayyana cewa wannan jarajin da ake shirin fara tatsa daga yan Najeriya zalunci ne, kuma ba za ta suba ido tana kallo ba.

Yan kwadagon sun ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ta janye harajin ko kuma su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262