Kungiyar TUC Ta Ja Daga, Ta Ba Gwamnatin Tinubu Kwanaki 14 Ta Janye Harajin Fetur

Kungiyar TUC Ta Ja Daga, Ta Ba Gwamnatin Tinubu Kwanaki 14 Ta Janye Harajin Fetur

  • Kungiyar kwadagon ma'aikata, TUC ta bayyana harajin da gwamnatin tarayya ta dora a kan fetur a matsayin zalunci
  • TUC ta ce ’yan Najeriya ba za su ci gaba da zama abin gwajin manufofin tattalin arziki a kasar nan ba
  • 'Yan kasuwan sun umarci rassanta a jihohi da su zauna a cikin shirin ko ta kwana bayan kwanaki 14 da su ka sanar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Kungiyar ƙwadago ta Trade Union Congress (TUC) ta yi fatali da shirin gwamnatin tarayya na ƙara harajin 5% a kan man fetur.

'Yan kasuwan sun bayyana karin a matsayin mugun abu da ke nuna rashin tausayi a tsarin tattalin arzikin ƙasar nan.

TUC ta fusata da haraji a kan man fetur
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ce an yi ƙarin harajin domin samar da ci gaba mai ɗorewa wajen manyan ayyuka a kasar nan.

Kara karanta wannan

"Ba ruwan Tinubu," An jingina harajin fetur da gwamnatin marigayi Umaru Yar'adua

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar TUC ta fusata da harajin man fetur

The Guardian ta wallafa cewa Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan tsarin haraji da gyaran manufofin kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce kasashen duniya 150 na aiwatar da wannan tsari.

Sai dai a wata sanarwa da shugaban TUC, Festus Osifo, da Sakatare janar, Nuhu Toro, suka rattaba wa hannu a madadin ƙungiyar, harajin da aka dora wa 'yan Najeriya ya yi yawa.

Ya ce:

“Wannan shiri ba wani abu ba ne illa zalunci a tsarin tattalin arziki da ke cutar da ’yan Najeriya da ke fama da matsin rayuwa."
“Har yanzu, ma’aikata da ’yan ƙasa na cikin radadin cire tallafi, tsadar mai, hauhawar farashin abinci, da faduwar darajar Naira. Yanzu kuma a ƙara musu haraji? Wannan na nufin ƙara jefa su cikin talauci ne da kuncin rayuwa.”

TUC ta ba gwamnati wa'adin kwanaki 14

TUC ta bayyana cewa idan gwamnati ba ta janye wannan shirin cikin kwanaki 14 ba, to za su tilasta daukar mataki, ciki har da yajin aiki na ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fadi tsoron da APC ta ji bayan kai wa 'yan adawa hari a wajen ibada

TUC ta ba gwamnati wa'adin janye harajin kayayyakin man fetur
Shugaban TUC, Osifo da na NLC Joe Ajaero Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Source: Twitter

Kungiyar ta ce:

“Mun umarci dukkannin rassanmu a jihohi da ƙananan hukumomi su kasance cikin shiri, kuma su jira umarni na gaba. Idan gwamnati ta ƙi sauraron kukan jama’a, za mu ɗauki matakin da ya dace.”

Kungiyar ta kuma nemi haɗin guiwa daga ƙungiyoyin farar hula, ƴan kasuwa, malamai, ɗalibai, da shugabannin addinai da su tashi tsaye wajen ƙin amincewa da wannan shiri.

An dora wa 'yan Najeriya harajin man fetur

A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya na iya amince wa da sabon tsarin haraji na ƙara 5% ga kayayyakin mai a fadin kasar nan daga shekarar 2026.

Wannan na nufin cewa za a ƙara wa kowace lita man fetur da aka sayar daga N900 zuwa N945—ma’ana ƙarin N45 ga kowace lita—idan aka fara aiwatar da dokar.

Ba a ayyana takamaiman ranar da za a fara aiwatar da wannan haraji ba, saboda gwamnati na jiran sahalewar Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng