Sawun Giwa: Masarauta Ta Ƙwace Sarautar da Aka ba Tinubu, Ta Faɗi Manyan Dalilai
- Majalisar sarakunan gargajiya ta Idoma ta yi zama kan sarautar da aka ba shugaban kasa, Bola Tinubu a jihar Benue
- An ji majalisar ta soke sarautar da aka ba Bola Tinubu da wasu mutum hudu a bikin Igede Agba na Benue da aka gudanar
- Shugaban majalisar, Och’Idoma V, ya ce karramawar ta sabawa umarnin da suka bayar a baya na dakatar da ba da sarauta a yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Majalisar sarakunan gargajiya ta Idoma a jihar Benue ta koka kan sarauta da aka ba Shugaban Najeriya watau Bola Tinubu.
Majalisar ta bayyana cewa ba ta amince da sarautar da aka ba Tinubu da wasu mutane hudu a bikin Igede Agba a karamar hukumar Oju ta jihar Benue ba.

Kara karanta wannan
An tsinci gawa gefen ofishin sakataren gwamnatin Tinubu, majalisa ta yi karin haske

Source: Twitter
Tinubu ya samu sarautar gargajiya a Benue
Rahoton Punch ya ce an mika sarautar ga Shugaban kasa ta hannun Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na cikin amincewar Mai Martaba Adiharu na Igede, CP Oga Ero (mai ritaya) ya bayar a ranar Asabar 6 ga watan Satumbar 2025.
A wurin bikin, an karrama wasu manyan mutane hudu da irin wannan sarauta a gaban jama’a da suka taru domin shagalin.
Dalillin kwace sarautar da aka ba Tinubu
Sai dai a sanarwar da ta fitar ranar Litinin, majalisar da shugabanta, Och’Idoma V, Dr. Elaigwu Odogbo John ke jagoranta, ta ce karramawar ta sabawa dokar da suka tsayar.
Sanarwar da sakataren majalisar, Mista Adegbe Uloko ya sanya wa hannu, mai taken “Soke Karramawar Sarautu da Igede Ta Bayar,” ta tabbatar da sabawa umarninsu na 2 ga Satumbar 2025.
Majalisar ta ce:
“Sarauta da Masarautar sarakunan gargajiya da Igede ta bayar a ranar 6 ga Satumba, 2025, ya sabawa dokar Majalisar Gargajiya ta Idoma, wannan karramawar ba ta da inganci.”

Source: Twitter
Masarauta ta yi gargadi kan ba Tinubu sarauta
Masarautar ta kuma jaddada cewa ita ce kadai majalisar gargajiya da gwamnati ta amince da ita a yankin Idoma, kuma ta ce duk wanda ya saba dokarta, ya saba ka'ida.
Don haka ta bukaci jama’a, hukumomi da sauran shugabannin gargajiya su yi watsi da sarautar da aka ba Shugaba Tinubu da sauran mutanen.
Sanarwar ta ce:
“An yi wannan jawabi ne domin kare mutuncin masarautun gargajiya a jihar Benue, da kiyaye doka, zaman lafiya da hadin kai.”
Majalisar ta bayyana cewa makon da ya gabata ta sanar da dakatar da bayar da kowace irin sarauta a fadin yankin domin tsaftace tsarin gaba daya, Leadership ta tabbatar da labarin.
An ba Tinubu sarauta a Akwa Ibom
Kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu sarautar gargajiya mafi girma a jihar Akwa Ibom da ke yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan
Tinubu ya waiwayi daliban da aka sace lokacin Jonathan, ya ba su tallafin N1.85bn
Sarakunan gargajiya na jihar sun mika sarautar a fadar shugaban kasa tare da tawagar da Gwamna Umo Eno ya jagoranta.
Tinubu ya bukaci hadin kan ‘yan siyasa don ciyar da kasa gaba, yana mai yabawa ci gaban da ake samu a Akwa Ibom domin samun bunkasar al'adu da tattalin arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
