Romon Siyasa: Kansila Ya Naɗa Sababbin Hadimai 18, Ya Raba Masu Wurin Aiki a Kaduna

Romon Siyasa: Kansila Ya Naɗa Sababbin Hadimai 18, Ya Raba Masu Wurin Aiki a Kaduna

  • Matasa 18 sun fara sharbar romon dimokuradiyya bayan da kansilan Kinkiba ya nada su masu ba shi shawara na musamman
  • Hon. Sanusi Hashim ya ce sababbin hadiman nasa, za su taimaka wajen bunkasa gundumar Kinkiba da ke karamar hukumar Soba
  • Daga cikin wadanda aka nada, akwai mai ba da shawara kan dattawa, harkokin kudi, matsalolin jama'a da sauran bangarori

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Wani kansila mai wakiltar mazabar Kinkiba a majalisar ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna, Sanusi Hashim, ya naɗa hadimai 18.

Hon. Sanusi Hashim, ya ce sababbin masu ba shi shawara na musamman, za su tallafa masa wajen kawo ci gaba ga gundumar Kinkiba.

Kansila ya nadimai masu ba shi shawara na musamman 18 a Kaduna
Dandazon 'yan jam'iyyar APC a wani taro, da kansilan Kaduna, Sanusi Hashim, yana jawabi. Hoto: @GoziconC/X, Sanusi Hashim/Facebook
Source: Twitter

Kansila a Kaduna ya nada hadimai 18

An rantsar da masu ba da shawarar a ranar Lahadi a wani taron da aka gudanar a makarantar firamare ta L.E.A., Kinkiba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Kano ya gana da Sheikh Jingir kan rasuwar malamin Izala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce taron ya samu halartar manyan jami’an jam’iyyar APC, magoya bayan jam’iyyar, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, da sauran al'ummar gundumar.

Hon. Sanusi Hashim ya bayyana cewa ya yi naɗin mukaman ne bisa cancanta, kuma yana da yakinin za wadanda ya nada zasu kasance masu sadaukarwa, biyayya, da yin ayyukan da za su kawo ci gaban gundumar Kinkiba.

"Ina kira gare su da su yi aiki da gaskiya, mutunci, rikon amana, da kuma tausayi ga mutanen wannan gunduma ta mu."

- Hon. Sanusi Hashim.

Kansila ya yaba wa Gwamna Uba Sani

Kansilar gundumar ta Kinkiba, ya ci gaba da cewa:

"Burina shi ne mu yi aiki tare a matsayin tawaga mai karfi, wacce za ta samar da ci gaba ga al'ummarmu da kuma cigaba ga babbar jam'iyyarmu ta APC."

Ya kuma nuna godiyarsa ga Gwamna Uba Sani bisa goyon baya da yake ba kansilolin kananan hukumomi a faɗin jihar, musamman ta hanyar samar da takin zamani don rarraba wa manoma.

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Ya yi alkawarin cewa, majalisar zartarwarsa za ta yi aiki tare da gwamnan wajen ganin an aiwatar da ayyukan cigaba ga al'ummar Kinkiba.

Sanusi Hashim, kansilan Kaduna ya ce za su ci gaba da marawa Uba Sani baya.
Kansilan gundumar Kinkiba, karamar hukumar Soba, jihar Kaduna, Hon. Sunusi Hashim. Hoto: Sunusi Hashim
Source: UGC

Sunayen hadimai 18 da kansilan ya nada

Legit Hausa ta tattaro sunayen sababbin hadiman kansilan da suka hada da:

  1. Shafiu Nuhu (Ayyuka)
  2. Shafiu Alhassan (Ci gaban jama'a)
  3. Shitu Ahmad (Babban sakatare - PPS)
  4. Alh. Isiya Yusuf Danju (Harkokin kuɗi)
  5. Danlarai Habibu (Alaƙa da masu ruwa da tsaki)
  6. Ibrahim Sufiyan (Alaƙa da jam’iyyu)
  7. Abbas Jafar (Matsalolin jama'a)
  8. Jibrin Lawal (Ci gaban harkokin noma)
  9. Aina’u Kabir (Harkokin mata)
  10. Sale Abdurrahman (Harkokin jama'a)
  11. Umar Shitu (Harkokin siyasa)
  12. Tasiu Umar (Yaɗa labarai)
  13. Salisu D. Tela (Kiwon lafiya)
  14. Yusuf Abdulkareem (Dattawa)
  15. Buhari Abubakar (Ilimi)
  16. Hamisu Salisu (Sakataren Tawaga)
  17. Dahiru Yau (Jami’in hulɗa da jama’a)
  18. Yahaya Kinkiba (Matasa)

An cafke kansilan Kinkiba da bindigar AK-47

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an tsaro a yankin Galadimiwa, karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna sun cafke Hon. Abdul Adamu Kinkiba.

Hon. Abdul, wanda a lokacin shi ne kansilan gundumar Kinkiba, ya shiga hannun jami'an tsaro, bayan da aka kama shi da bindiga kirar AK-47.

Da ake yi masa tambayoyi, Abdul Kinkiba ya shaidawa jami’an tsaron cewa wani mutum ne ya ba shi bindigar, da zummar kai wa wata dabar 'yan ta'adda.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com