Shettima Ya Yi Alhini kan Kisan Boko Haram, Ya Ba da Tabbacin Yin Adalci
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a jihar Borno, inda suka hallaka sojoji da fararen hula
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya nuna alhininsa kan danyen aikin da 'yan ta'addan su ka yi kan bayin Allah
- Shettima ya nuna cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da samar da zaman lafiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana alhininsa kan harin ta’addanci da 'yan Boko Haram suka kai a kauyen Darajamal, jihar Borno.
Harin na 'yan ta'addan Boko Haram ya jawo asarar rayuka da dama ciki har da na fararen hula da sojoji.

Source: Twitter
Hadimin Shettima kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha, ne ya sanya sakon ta'aziyyar mataimakin shugaban kasan a shafinsa na X.
Me Shettima ya ce kan harin Boko Haram?
Kashim Shettima ya bayyana harin a matsayin babban bala’i ga kasa, yana mai cewa kisan ya jefa Najeriya baki ɗaya cikin zaman makoki.
"Ina miƙa ta’aziyyata ga Gwamna Babagana Umara Zulum, jama’ar jihar Borno da rundunar sojojin Najeriya kan wannan mummunan rashi na ‘yan uwanmu."
"Wannan mutuwa ta jefa ƙasa baki ɗaya cikin bakin ciki, amma muna da yakinin adalci zai tabbata ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu."
- Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasan ya tabbatarwa mazauna jihar cewa gwamnatin tarayya, karkashin shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da cikakkiyar aniyar kawar da ta’addanci.
Ya tunatar da umarnin shugaban kasa ga sojojin Najeriya kan sake duba dabarun tsaro na yanzu tare da tura sababbin kayan yaki na zamani da na’urorin leken asiri domin karfafa yaki da kungiyoyin ta’addanci a faɗin kasar nan.
Gwamnati za ta samar da 'yan sandan jihohi

Kara karanta wannan
"Ku tashi ƴan Najeriya," Atiku ya zaburar da jama'a kan kisan kiyashin Boko Haram
Kashim Shettima ya kuma jaddada cewa gwamnati tana la’akari da kafa ‘yan sandan jihohi.
Ya ce za a samar da su ne bisa ga matsayar Shugaba Tinubu cewa akwai matsalolin tsaro da ke rundunoni na musamman masu fahimtar yanayi da al’adun yankin domin kare al’umma yadda ya kamata.

Source: Twitter
A ranar Asabar, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci kauyen Darajamal domin yin ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa sakamakon harin Boko Haram na daren Juma’a.
Mataimakin shugaban kasan ya kuma yi addu’a domin samun rahamar Allah ga rayukan waɗanda suka mutu, tare da tabbatar wa al’ummar Borno cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa musu har sai an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Yadda 'yan Boko Haram suka kashe mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun hallaka mutane 63 a jihar Borno.
Mutanen da suka tsira daga harin sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun fafata da dakarun sojoji, kafin daga karshe su fatattake su.
Sun bayyana cewa miyagun sun rika shiga gida-gida sun harbe manyan maza da suka yi arba da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
