Talauci Ya Addabi Sokoto, za a Dauki Ma'aikata domin Rage Fatara da Yunwa
- Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince da kafa kwamiti na musamman don ɗaukar ma’aikatan gwamnati
- Rahoto ya nuna cewa kafa wannan kwamiti na daga cikin matakan rage zaman kashe wando da rashin aikin yi a jihar
- An ba wa kwamitin wata ɗaya ya kammala rahoton ayyukansa tare da ba da shawarwari kan yadda aikin zai gudana
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Gwamnatin jihar Sokoto ta ce ta dauki sabon mataki domin magance zaman kashe wando da matsalolin rashin aikin yi a tsakanin matasa ta hanyar ɗaukar ma’aikata.
Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya amince da kafa wani kwamiti na musamman da zai tsara tsarin ɗaukar ma’aikata domin bai wa ‘yan asalin jihar dama su samu aikin gwamnati.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa sanarwar hakan ta fito ne daga gidan gwamnati Sokoto, ta hannun jami'in yada labarai na jihar Abubakar Bawa.

Kara karanta wannan
Tinubu zai kawo tsarin aiki da ba a taba yi ba a Najeriya, komai zai sauya a ofisoshi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kafa kwamitin daukar ma'aikata a Sokoto
A cewar sanarwar, an kafa kwamitin daukar ma'aikatan ne da nufin dakile abubuwan da ke haifar da zaman kashe wando da shigar matasa harkokin rashin tsaro.
Hakan ya haɗa da rage tasirin masu bayar da bayanan sirri ga ‘yan ta’adda da sauran miyagu a fadin jihar.
Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin Jelani Kalgo, tare da wasu fitattun ‘yan jihar da suka haɗa da Sahabi Isa Gada, Bature Shinkafi da Muhammad Bello Nagwari.
Haka zalika, kwamishinoni biyu; Ladan Ala na ma'aikatar Ilimi da Faruk A. Wurno na harkar Lafiya za su kasance cikin kwamitin.
Haka kuma, manyan sakatarorin hukumar Ma’aikata da ta Kananan Hukumomi za su kasance cikin kwamitin, yayin da Gandi Umar Muhammad zai kasance a matsayin sakatare.
Ayyukan da aka daura wa kwamitin
An bayyana ayyukan da aka daura wa kwamitin da suka haɗa da samar da ƙa’ida ta musamman da za a bi wajen tantance mutanen da suka cancanci samun aikin gwamnati a jihar.
Bayan haka, kwamitin zai gudanar da tambayoyi da tantancewar ƙwarewa ga waɗanda aka zaɓa domin tabbatar da cancantarsu.
Daga ƙarshe, kwamitin zai gabatar da sunayen waɗanda suka cancanta don amincewar gwamnati da kuma bayar da rahoton cikakken aikin da aka yi cikin wa’adin wata guda.

Source: Facebook
Matakin rage rashin aikin yi
A cewar gwamnatin jihar, wannan sabon mataki zai taimaka wajen samar wa da matasa aikin yi, rage zaman kashe wando da kuma bai wa jama’a damar taka rawar gani a cigaban jihar.
Gwamna Aliyu ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su magance rashin aikin yi da kuma dakile matsalolin tsaro da suka addabi al’umma.
Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto na jaridar the Cable ya nuna Sokoto a matsayin jihar da ta fi talauci yayin da Bayelsa da Gombe ke binta a baya.
Za a koya wa 'yan Najeriya hada mota
A wani rahoton, kun ji cewa za a koya wa 'yan Najeriya 2,000 gyara da hada motoci masu aiki da lantarki.
Rahotanni sun bayyana cewa za a yi shirin ne kyauta domin sama wa matasan ayyukan da za su haba tattalin kasa.
Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin matasa ya yaba da matakin, inda ya ce matasan za su zama abin alfahari ga kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

