Boko Haram: Tinubu Ya ba da Umarnin Gaggawa bayan Kisan Mutum 63 a Borno

Boko Haram: Tinubu Ya ba da Umarnin Gaggawa bayan Kisan Mutum 63 a Borno

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar soji da su sake duba dabarun tsaro a ƙasar nan bayan mummunan harin Boko Haram
  • Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana sakon Tinubu ta cikin sanarwar da ya fitar bayan kisan mutum 63 a Borno
  • Shettima ya nanata kudirin Bola Tinubu na kokarin samar da 'yan sandan jihohi domin a ci galabar matsalar tsaro a sassan Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni ga rundunonin tsaron Najeriya a kan su sake duba dabarun yakinsu.

Ya bukaci su sake inganta matakan da su ke bi wajen yaki da ta’addanci a ƙasar nan, daga ciki har da amfani da sababbin kayan aikin soji da na leƙen asiri.

Kara karanta wannan

"Ku tashi ƴan Najeriya," Atiku ya zaburar da jama'a kan kisan kiyashin Boko Haram

Shugaba Tinubu ya ba sojoji umarni
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Shugaban ya bayar da wannan umarni ne ta cikin sanarwar da ofishin Mataimakinsa, Kashim Shettima ya fitar.

Bola Tinubu ya mika ta'aziyya Borno

Jaridar Punch ta wallafa cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana ta’aziyya gwamnati ga jihar Borno.

Haka kuma ya mika gaisuwa ga al’ummar jihar bisa mummunan harin da aka kai wa al’ummar Darajamal da ke ƙaramar hukumar Bama.

Rahotanni sun bayyana cewa mayakan Boko Haram sun yi wa kauyen kofar rago, inda su ka kashe mutane akalla 63.

Mutanen da aka kashe sun hada da fararen hula da kuma sojojin da aka fara fafata wa da su a wajen gari kafin Boko Haram ta kutsa kauyen.

Gwamnatin Tinubu ta dauki mataki

A cewar Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Shettima ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ta dauki mataki.

Daga cikin matakan, ta amince a samu karin jiragen leƙen asiri da kuma umarnin duba tsare-tsaren tsaro domin tabbatar da shawo kan matsalar tsaro a ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

"A koresu": Kungiyar 'yan Arewa ta ba Tinubu shawara kan rashin tsaro

Kashim ya mika ta'aziyyar Tinubu ga jama'ar Borno
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Ya ce:

"Ina mika ta’aziyya ta ga Gwamna Babagana Umara Zulum, al’ummar Borno da kuma dakarun soji bisa wannan babban rashi. Wannan hari ya girgiza al’umma baki ɗaya."

Shettima ya bayyana kwarin gwiwarsa ga rundunonin tsaro kan iya magance kalubalen tsaro da ke addabar jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya tana duba yiwuwar kafa ‘yan sanda na jihohi domin su fahimci ƙasa, al’adu da mu’amala da al’umma yadda ya kamata.

Atiku ya mika ta'aziyya ga jama'an Borno

A baya, mun wallafa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya bayyana alhini da takaicinsa kan sabon harin Boko Haram a Borno da ya hallaka mutum 63.

Atiku ya bayyana cewa wannan hari na Boko Haram wani babban tunatarwa ce na yadda rayukan ‘yan Najeriya ke ci gaba da salwanta ba tare da laifin komai ba.

'Dan siyasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada karfi da karfe wajen yaki da ta’addanci tare da goyon bayan kokarin jami’an tsaro domin tsaron rayukansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng