"Ku Tashi Ƴan Najeriya," Atiku Ya Zaburar da Jama'a kan Kisan Kiyashin Boko Haram

"Ku Tashi Ƴan Najeriya," Atiku Ya Zaburar da Jama'a kan Kisan Kiyashin Boko Haram

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da sabon harin da mayakan Boko Haram su ka kai Borno
  • Ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su tashi tsaye wajen yaƙi da ta’addanci domin a kawo karshen kisan gillar 'yan ta'adda
  • Atiku ya yi ta’aziyya ga gwamnan Borno, Babagana Zzulum da iyalan mutanen da Boko Haram ta kashe a karshen makon jiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da sabon harin Boko Haram da ya kashe mutane da dama a ƙauyen Darajamal, jihar Borno.

Ya ce dole ne a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen fuskantar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya domin dakile cin mutuncin bayin Allah da 'yan ta'adda ke yi.

Kara karanta wannan

Yaron El Rufa'i: Uba ya yi raddi ga kalamai da zarge zargen tsohon Gwamnan Kaduna

Atiku Abubakar ya yi ta'aziyya ga jama'ar Borno
Hoton Atiku Abubakar a yayin wani taro Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya bayyana takaicinsa tare da mika ta'aziyya a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Atiku ya zaburar da jama'a kan Boko Haram

Atiku Atiku ya bayyana cewa wannan kashe-kashe da aka yi a jihar Borno tunatar wa ce a kan yadda ake salwantar da bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ya bayyana cewa:

“Wannan tashin hankalin marar ma’ana tunatarwa ce mai game da asarar rayukan da jama'armu ke ci gaba da fuskanta saboda ta’addanci.”

Ya ƙara da cewa ya kamata jama'a su taimaka wa kokarin sojoji da sauran jami'an tsaro domin a kawo karshen wannan kashe-kashe.

Atiku Abubakar ya nemi a taimaka wa sojoji

Tsohon 'dan takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya kamata jama'a su mutunta sadaukarwar da sojoji da fararen hula ke yi.

Ya nemi al'umma su ƙarfafa tsaron unguwanni, ƙara haɗin kai, da kuma jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya kadu kan harin Boko Haram, ya fadi barnar da aka yi

Atiku ya nemi a taimaka wa sojoji
Hoton gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Source: Facebook

Ya ce:

“Ya kamata mu tashi tsaye wajen fuskantar wannan barazana cikin haɗin kai.”

Ya bayyana cewa ya yi matuƙar kaduwa da kisan mutane da dama ciki har da jaruman sojoji a harin da ya auku a Darajamal.

Atiku ya ce:

“Ina mika ta’aziyyata ga iyalan waɗanda suka rasu, ga jama’ar Borno masu juriya, da kuma Gwamna Babagana Zulum, wanda gaggawar da ya yi na kai ziyara wurin al’ummar da abin ya shafa abin yabawa ne.
"Allah SWT Ya ji kan waɗanda suka rasu, Ya ba su Aljanna Firdaus, ya kuma ba iyalansu haƙuri.”

Boko Haram ta kashe jama'a a Borno

A wani labarin, mun wallafa cewa akalla mutane 63 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai kauyen Borno.

A cewar mazauna yankin da suka tsira daga harin, ‘yan ta’addan sun mamaye kauyen ne da daddare a ranar Juma’a, 5 ga watan Satumban 2025.

Wadanda suka tsira sun bayyana cewa kafin kai harin, ‘yan ta’addan sun fara fafatawa da dakarun sojoji a wajen kauyen, daga baya kuma su ka afka masu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng