"An Yi Ta'addanci": Yadda 'Yan Boko Haram Su Ka Kashe Mutane 63 a Jihar Borno

"An Yi Ta'addanci": Yadda 'Yan Boko Haram Su Ka Kashe Mutane 63 a Jihar Borno

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun ci karensu babu babbaka bayan sun kai wani harin ta'addanci a jihar Borno
  • Miyagun sun yi artabu da jami'an tsaro kafin daga bisani su rika shiga gida-gida suna kashe bayin Allah
  • Wadanda suka tsira daga harin sun bayyana yadda lamarin mara dadin ji ya auku a karamar hukumar Bama

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Mutanen da suka tsira sun ba da labarin yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe mutum 63 a Borno.

'Yan ta'addan sun kashe mutanen ne a wani hari da suka kai kauyen Darul Jamal da ke karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe mutane a Borno
Hoton gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a cikin ofis Hoto: @GovBorno
Source: Facebook

A wata hira da jaridar Daily Trust ta yi da su, mazauna yankin sun ce ‘yan ta’addan sun mamaye kauyen ne a daren ranar Juma’a, 5 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan Boko Haram suka yi barna a Borno

'Yan ta'addan sun fara fafatawa da sojoji kafin daga baya su afka kan fararen hula.

Sun danganta harin da karancin jami’an tsaro a yankin.

Sai dai, wata majiya daga jami’an tsaro ta musanta wannan zargi, tana mai cewa an tura isassun dakarun sojoji a yankin kuma sun sha dakile hare-haren ‘yan ta’adda a baya.

“A wannan hari, ‘yan ta’addan sun kawo farmaki sau uku a jere kafin daga bisani su fatattaki sojoji daga sansaninsu."
"Sun kwashe motoci masu dauke da bindigu guda biyu, babura uku mallakar CJTF, sannan suka kona kyamarorin CCTV da na’urorin sadarwa na rediyo."

- Wata majiya

An kashe sojoji da fararen hula

Ya kara da cewa sojoji biyar da fararen hula 58 aka kashe a harin. Daga cikin fararen hular akwai leburori, direbobi da kuma waɗanda suka dawo daga gudun hijira.

Maharan sun sace makamai da alburusai wadanda sojojin da suka gudu suka bari kafin su kona wuraren da su ke zama.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya kadu kan harin Boko Haram, ya fadi barnar da aka yi

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Hassan Kolo, ya ce sojojin ne suka fara gargadinsu game da harin Boko Haram mintuna kaɗan kafin ‘yan ta’addan su iso.

“Sojojin sun ce suna cikin musayar wuta da ‘yan ta’addan, kuma suka shawarcemu mu shiga gidajenmu mu kulle ƙofofi. Mun yi hakan."
"Abin takaici, ‘yan ta’addan sun rinjayi sojoji sannan suka mamaye gidajenmu. Suna shiga gida-gida suna kashe manyan maza da su ka gani, sannan suna kona gidaje."
"Sun kona gidaje 24. Allah ya taimake ni na gudu cikin daji na ɓuya, shi ne ya sa na tsira."

- Hassan Kolo

Wadanda suka tsira sun yi bayani

Wani wanda ya tsira daga harin, Modu Abdul, ya ce jami'an CJTF sun fara kokarin dakatar da ‘yan ta’addan kafin daga bisani suka fara shiga gida-gida suna kashe mutane.

'Yan Boko Haram sun kashe mutane a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original
"Amma ba a dade ba, harsasan CJTF suka kare wanda hakan ya sa suka ja da baya. Aka bar mu sai mu kadai, sai ‘yan ta’addan suka yi abin da suka ga dama, suna shiga gida-gida suna kashe maza."
"Mun lura sun tafi ne bayan karfe 11:00 na dare. Babu jami’in tsaro da ya dawo har sai da gari ya waye.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, an samu asarar rayuka

- Modu Abdul

An ji ta bakin jami'an 'yan sanda

Da aka nemi jin ta bakin jami’an tsaro game da karancin tsaro a yankin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce ba karkashin ikonsu Darul Jamal yake ba.

ASP Nahum Kenneth Daso ya ce kauyen yana karkashin ikon sojoji ne.

Sojojin sama sun hallaka 'yan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya aun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a Borno.

Sojojin sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'addan na Boko Haram a maboyarsu da ke cikin dajin Sambisa.

Bama-baman da jiragen yaki na sojojin saman su ka jefa musu, sun yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda guda 15.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng