‘Abin da ba a Sani Ba’: Musulman Kudancin Kaduna Sun Tono Cin Kashi da Ake Yi Musu
- Al'ummar Musulmi a Kudancin jihar Kaduna sun yi zarge-zarge kan matsin lamba da suke fuskanta
- Ƙungiyar Concerned Muslim Ummah ta zargi wasu shugabanni da sauya tarihi, cin moriyar rikici da nuna wariya
- Ta ce Musulmi sun kai kusan kashi 40 cikin ɗari a yankin, tana jaddada cewa rikice-rikicen Kudancin Kaduna sun daɗe suna faruwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Ƙungiyar Musulmi ta Kudancin Kaduna ta yi tone-tone kan wasu abubuwa da suke faruwa a yankin.
Kungiyar mai suna “Concerned Muslim Ummah” ta ce wasu manyan mutane na yankin suna amfani da tarihi da siyasa wajen raba kan al'umma.

Source: Original
Hakan na cikin wata sanarwa a taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Kaduna wanda Aminiya ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yawan korafi daga Musulman Kudancin Kaduna
Wannan ba shi ne karon farko da Musulman Kudancin Kaduna ke kokawa kan nuna musu wariya saboda yankin da suka fito.
Ko a farkon mulkin Uba Sani, wata kungiya ta fito ta kalubalanci gwamnan game da nuna wariya a mukamansa.
Kungiyar matasa Musulmai daga Kudancin Kaduna sun koka kan yadda aka nuna musu wariya a mukaman Gwamna Uba Sani.
Jam'iyyar da Musulman Kaduna za su zaba
Sakataren kungiyar, Shu'aibu Abdallah shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 28 ga watan Agustan 2023 a Kaduna.
Ya ce Musulman Kudancin Kaduna gaba dayansu APC su ka zaba duk da kalubalen da su ke fuskanta a yankin.
Sun bukaci shawo kan matsalolin da suke fuskanta domin samun daidaito a mulki da ci gaban kasa.

Source: Facebook
Yawan Musulmi a yankin Kudancin Kaduna
Kungiyar Musulmi ta ƙaryata ikirarin da ake yi cewa Kudancin Kaduna na da Kiristoci kawai, tana bayyana hakan a matsayin kuskure.
Ta ce Musulunci ya dade da kafuwa a yankin tun ƙarni da dama da suka gabata, inda ta bayyana Musulmi sun kai kashi 40 cikin ɗari.
Ƙungiyar ta ce rikice-rikice kamar na Zangon Kataf a 1992 da na zaben 2011 sun nuna cewa matsalolin yankin ba sababbi ba ne.
Kungiyar ta kwarara yabo ga Uba Sani, Tinubu
Haka kuma ta ce akwai manyan da ke cin gajiyar rikice-rikicen, suna nuna wariya ga Musulmi a masarautu da ƙirƙirar adadin jama’a da ba gaskiya ba.
Ta yaba wa Gwamna Uba Sani da Shugaba Tinubu bisa goyon bayan Musulmi a zaɓen 2023 da ya gabata.
Kungiyar ta kuma tura roƙo na musamman ga gwamnati da kafafen labarai su guji siyasar rarraba kawunan al'umma.
Yan Kudancin Kaduna sun soki mulkin El-Rufai
Mun ba ku labarin cewa Ƙungiyar SKLC ta mutanen Kudancin jihar Kaduna na son a binciki tsohon Gwamna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai.
Ƴan ƙungiyar sun zargi tsohon gwamnan na jihar Kaduna da yin mulkin zalunci tare da takurawa mutanen Kudancin Kaduna.
Sun buƙaci hana shi sake riƙe wani muƙami saboda abin da suka kira gallazawa mutanen yankin da ya yi a lokacin mulkinsa.
Asali: Legit.ng

