Tirkashi: Gwamna Zai Gyara Titi 1 kan Naira Biliyan 6.5, An Zabi Ɗan Kwangila

Tirkashi: Gwamna Zai Gyara Titi 1 kan Naira Biliyan 6.5, An Zabi Ɗan Kwangila

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya amince da kashe N6.5bn don faɗaɗa titin garin Misau mai tsawon kilomita 7.5
  • Gwamnatin Bala ta dauki nauyin aikin ne domin rage cunkoson ababen hawa da hadura a garin Misau, da ke da tasiri a jihar
  • Injiniyan da ke kula da aikin, Nicholas David ya fadi lokacin da ake sa ran kammala aikin da dan kwangilar da zai yi aikin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da kashe N6.5bn don faɗaɗa titin garin Misau mai tsawon kilomita 7.5 da ke a karamar hukumar Misau.

Aikin fadada titin garin Misau wani bangare ne na kokarin gwamnatin Bala Mogammed na inganta ababen more rayuwa, hanyoyin zirga-zirga, da kuma rage hadurran mota.

Gwamna Bala zai kashe N6.5bn a gina titi a Misau da ke jihar Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, yana jawabi a wani taro a gidan gwamnati. Hoto: @SenBalaMohammed/X
Source: Twitter

Misau, wata muhimmiyar cibiyar kasuwanci ce kuma gari ne mai zaman kansa a kan babban titin Bauchi–Azare, wanda ya daɗe yana fama da cunkoson ababen hawa da kuma yawan hadurra saboda rashin fadin hanya, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bauchi: Lokacin kammala aikin titin Misau

Kamfanin da aka ba kwangilar gudanar da aikin, Mother Cat, ya tabbatar da cewa za a kammala titin kafin karshen shekarar 2025.

A lokacin da yake duba wurin aiki a ranar Asabar, injiniyan aikin, Nicholas David, ya ce an riga an kammala fiye da kashi 50 cikin 100 na aikin.

David ya ce:

“Kamar yadda kuka gani, muna iyakar kokarinmu kuma aikin yana ci gaba. Mun yi fiye da rabi, kuma ana samun ci gaba a sauran rabin.”

Ya kuma yi bayanin cewa aikin ya samu tsaiko saboda hauhawar farashin kayan gini, amma ya ce farashin ya daidaita, inda ya kawar da bukatar karin kudin aikin.

Ya kuma tabbatar da cewa kamfanin ya kuduri aniyar samar da ingantaccen aiki daidai da tanadin kwangilar.

Gwamnatin Bauchi ta gamsu da aikin gina titi

A nasa bangaren, wani jami’in da ke kula da aikin daga ma’aikatar ayyuka da sufuri ta jihar Bauchi, Injiniya Mohammed Babagana, ya yaba wa Mother Cat, inda ya tabbatar da cewa "an kammala fiye da rabin aikin."

Kara karanta wannan

Abinci: Kano, Gombe, jihohin Arewa 11 sun samu tallafin Amurka na ₦49.686bn

Babagana ya kara da cewa, “karuwar farashin kayayyaki ya tilasta wa kudin kwangilar zuwa N6bn,” amma ya tabbatar da cewa za a samar da ingantaccen aiki.

Duk da cewa titin ya na karkashin tarayya ne, ya ce gwamnatin Bauchi ta dauki nauyin aikin ne domin rage hadura da saukaka zirga-zirgar ababen hawa ga al’ummar Misau.

Kamfanin Mother Cat ya ce zai kammala aikin titin Misau nan da karshen shekarar 2025
Ma'aikata na aikin gina titi a wani sashe na Najeriya. Hoto: @FMWNIG
Source: UGC

Kokarin gwamnatin Bauchi kan titin Misau

An ruwaito cewa gwamnatin Gwamna Bala Mohammed ta ba da fifiko ga ci gaban tituna a matsayin wani ginshiki na tsarin samar da ababen more rayuwa.

Gwamnatin jihar ta dauki nauyin kudin aikin titin duk da matsayinsa na titin tarayya, hakan ya nuna jajircewarta wajen samar da ingantattun hanyoyi da kuma rage wa al'umma wahala.

Bayan kammala shi, ana sa ran hanyar mai tsawon kilomita 7.5 za ta rage cunkoso a garin Misau, da inganta tsaro, da kuma bunkasa tattalin arziki a karamar hukumar.

Gwamna ya kwace kwangilar titin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Kano ya soke kwangilar titin Jaba-Gayawa tare da mayar da Dakata-Yadakunya zuwa hannu biyu, a kan kudi N6.1bn.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya

Soke kwangilar ya biyo bayan bidiyon Dan Bello da ya nuna lalacewar titin na Kano, wanda ya jefa mazauna yankin cikin tsananin damuwa.

Gwamna Abba Yusuf ya kuma amince da kashe N14.8bn kan ayyukan da suka hada da gyaran asibiti, makarantu da sauran ababen more rayuwa a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com