Gwamna Zulum Ya Kadu kan Harin Boko Haram, Ya Fadi Barnar da Aka Yi

Gwamna Zulum Ya Kadu kan Harin Boko Haram, Ya Fadi Barnar da Aka Yi

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai wani sabon harin ta'addanci a karamar hukunar Bama ta jihar Borno
  • Tantiran 'yan ta'addan sun hallaka sojoji da fararen hula a yayin harin ta'addancin da su ka kai
  • Gamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci kauyen da lamarin ya auku, inda ya ganewa idonsa irin barnar da aka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nisha

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara kauyen Darajamal da ke karamar Bama, sakamakon harin Boko Haram.

Gwamna Zulum ya ziyarci kauyen ne domin jajantawa iyalan mutane 63 da 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe 63 a daren ranar Juma’a.

Gwamna Zulum ya nuna takaici kan harin Boko Haram
Hoton gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum Hoto: @GovBorno
Source: Facebook

Zulum ya kai ziyara kan harin Boko Haram

A cewar wata sanarwa da aka sanya a shafin gwamnan Borno na Facebook, Gwamna Zulum ya ziyarci kauyen ne a ranar Asabar, 6 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

"Yaudara ce": Gwamna Uba Sani ya fallasa 'yan siyasa kan matsalar rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda abin ya rutsa da su sun haɗa da sojoji biyar da kuma kusan fararen hula 58.

Fararen hular na daga cikin wadanda aka raba da muhallansu sakamakon hare-haren Boko Haram, sai dai sun koma Darajamal watanni biyu da suka gabata.

Gwamna Zulum, wanda abin ya taɓa shi sosai, ya gana da shugabannin al’umma tare da rarrashin iyalan da suka rasa ’yan uwansu.

Gwamna Zulum ya yi jaje

"Mun zo nan ne domin mu jajantawa jama’ar Darajamal bisa abin da ya faru daren jiya wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama."
"Abu ne mai matukar bakin ciki. Wannan al’umma an dawo da su ne watanni kaɗan da suka gabata suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum, amma abin takaici Boko Haram sun kai musu hari daren jiya. Ziyarmu ita ce don jajantawa tare da karfafa musu guiwa.”

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Game da waɗanda abin ya rutsa da su, gwamnan ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya kawo tsarin jawo hankalin yara shiga makaranta a Borno

"A wannan lokaci mun tabbatar cewa mutane 63 sun rasa rayukansu, sojoji da fararen hula, kodayake yawanci fararen hula ne.”

Zulum ya koka kan rashin tsaro

Zulum, yayin da ya bayyana ƙalubalen da ake fuskanta wajen yaƙi da rashin tsaro, ya kuma yi kira a hanzarta tura sababbin Forest Guards (masu gadin daji) da aka horar domin su taimakawa sojoji wajen kare al’umman da ke cikin haɗari.

Gwamna Zulum ya kai ziyara kan harin Boko Haram
Hoton Gwamna Zulum yayi ziyarar da ya kai kauyen Darajamal Hoto: @GovBorno
Source: Twitter
"Ya kamata mu lura cewa yawan sojojin da ake da shi bai wadatar don su kare ko’ina ba. Ya zuwa yanzu, an riga an horar da rukuni biyu na masu gadin daji."
"Don haka, ɗaya daga cikin hanyoyin da ya kamata a aiwatar nan da nan, shi ne a tura wadannan da aka horar zuwa mafi yawan wuraren da ke cikin haɗari, domin su kare dazuka da al’umman da ke cikinsu."

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Gwamna Zulum ya ba iyaye tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da ba iyayen daliban da suka bar 'ya'yansu shiga.makaranta tallafin kudi.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

Gwamna Zulum ya kuma amince da ba da abinci kyauta ga daliban wadanda suke zuwa makaranta.

Hakazalika ya koka kan yadda ba a samun yara na shiga makaranta a yankin Arewacin jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng