Gwamna Zulum Ya Kawo Tsarin Jawo Hankalin Yara Shiga Makaranta a Borno

Gwamna Zulum Ya Kawo Tsarin Jawo Hankalin Yara Shiga Makaranta a Borno

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan karancin daliban da ake samu a makarantu
  • Bisa hakan sai gwamnan ya kawo tsarin da zai jawo hankalin iyayen yara su rika tura yaransu zuwa makaranta
  • A bisa tsarin, iyayen dalibai za su samu tallafin kudi domin karfafa musu gwiwa su bar yaransu su ci gaba karatu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwarsa kan karancin yawan ɗaliban da ke shiga makarantar boko a wasu yankunan jihar.

Gwamna Zulum ya koka kan yadda ba a samun dalibai musamman a garin Gajiganna, inda yara 90 kacal aka yi wa rajista daga cikin jama’a kusan 50,000.

Gwamna Zulum ya ba dalibai tallafi a Borno
Hoton Gwamna Babagana Umara Zulum cikin aji tare da dalibai da lokacin da yake jawabi Hoto: @GovBorno
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Gwamna Zulum ya bayyana damuwar sa ne a ranar Juma’a lokacin da ya kaddamar da makarantar 'Higher Islamic College' a garin Gajiganna.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane sabon tsari Zulum ya fito da shi?

Domin magance wannan matsala, Gwamna Zulum ya amince da biyan kuɗin tallafi na N300,000 ga iyayen ɗaliban guda 90.

A bisa tsarin, za a ba da N250,000 ga kowanne daga cikin iyayensu maza, yayin da za a ba iyayensu mata N50,000.

Gwamna Zulum ya kuma bayar da umarnin samar da abinci kyauta a wannan makaranta da kuma a sauran makarantun da ke da karancin ɗalibai, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

A cewar gwamnan, wannan umarni na nufin kara yawan masu shiga makaranta a Arewacin jihar, yankin da ya sha fama da fitina sakamakon shafe fiye da shekara 10 yana fuskantar hare-haren 'yan ta'adda.

Ya jaddada bukatar ɗaukar matakai na musamman don bunkasa ilimi a Arewacin Borno, wanda ya fi kowanne yanki fama da matsalar ta'addanci.

Gwamnatin na son dalibai su samo ilmi

Ya kuma bayyana manufar gwamnatin jihar ta samar da ilimi mai zurfi ga ɗaliban Tsangaya, wanda ya haɗa ilimin addinin Musulunci da na boko.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fito ya fadi gaskiya, ya ce an kashe jami'an tsaro sama da 76

"Dole ne mu ɗauki matakan musamman don bunkasa ilimi a Arewacin Borno. Wannan shi ne yanki daya tilo a jihar da bai samu ci gaba a bangaren ilimi ba."
"Don haka, dukkan shugabannin hukumomin kula makarantun sakandare da na firamare suna nan, ina so ku maida hankali a Arewacin Borno."
"Za ku ga yadda a wannan gari da ke da jama’a kusan 50,000, ɗalibai 90 kacal aka yi musu rajista a makarantar sakandare."
"Dole mu tallafawa iyayen waɗannan ɗalibai 90 daga irin waɗannan garuruwa kamar Gajiganna. Abu ne wajibi mu tabbatar da cewa waɗannan ɗalibai sun kammala karatunsu, domin hakan babban ci gaba ne."
"Za mu amince da biyan N250,000 ga kowanne uba da N50,000 ga kowace uwa. Ga ɗaliban kansu kuma, za mu ware N50,000 kowane daga cikinsu domin tallafa musu wajen bukatun yau da kullum."

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Gwamna Zulum ya kaddamar da makaranta a Borno
Hoton Gwamna Zulum tare da jami'an gwamnati wajen kaddamar da makaranta a garin Gajiganna Hoto: @GovBorno
Source: Twitter

Gwamna Zulum ya yi wa Sowore martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umar Zulum, ya yi kan zarge-zargen da Omoyele Sowore, ya yi.

Gwamna Zulum ya musanta zargin cewa akwai wani dakin azabtarwa da ake tsare mutanen da suka yi laifi.

Hakazalika ya musanta zargin da Sowore ya yi kan cewa gwamnatinsa ta kashe biliyoyin kudi don kula da tubabbun 'yan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng