'Yan Bindiga Sun Yi Tsaurin Ido, Sun Tare Motar Gwammati cike da Mutane a Najeriya
- 'Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun tare motar Edo Line, kamfanin sufurin motoci na gwamnatin jihar Edo
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kwashe duka fasinjojin cikin motar, da na wasu motoci biyu a kan titin Benin zuwa Auchi
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Edo ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce jami'an tsaro sun ceto mutum 16 daga ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Wasu miyagun yan bindiga sun farmaki motar kamfanin sufurin Edo-Line, mallakin gwamnatin jihar Edo a titin Benin zuwa Auchi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa fasinjoji 18 da ke cikin sabuwar motar kirar Bas sun fada hannun maharan a jiya Juma'a, 5 ga watan Satumba, 2025.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mutanen da ke cikin motar bas din Edo Line na hanyarsu ta zuwa Abuja lokacin da suka fada tarkon 'yan bindigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun tare motar Edo Line
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun tare motar, sannan suka tilasta wa fasinjojin fitowa daga bas din Edo Line, suka iza keyarsu zuwa cikin daji.
An tattaro cewa sai da yan bindigar suka gama tafiya da mutanen cikin motar, sannan jami'an tsaro suka isa wurin.
Wani faifan bidiyo da da ake yadawa na wurin da lamarin ya faru ya nuna jerin motocin da suka tsaya a gefen duka bangarorin titin zuwa Auchi, in ji Daily Post.
Mutum nawa maharan suka sace a Edo?
A bidiyon, an ga sabuwar motar bas ta Edo Line a gefen titin babu kowa a ciki, da wasu motoci guda biyu da ake tsammanin yan bindigar sun tafi da mutanen ciki.
Har yanzu ba a san adadin mutanen da ke cikin sauran motocin biyu ba amma an ce motar Edo Line na dauke da fasinjoji 18 tare da direba, kuma maharan sun sace dukansu.
A makonnin da suka gaba ta ne Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da sababbin motocin kamfanin Edo Line, wanda Gwamna Monday Okpebholo ya sayo.

Source: Getty Images
Rundunar 'yan sanda ta fara ceto fasinjojin
Sai dai a ranar Asabar, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Edo, SP Moses Iyamu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa dakaru sun ceto mutane 16 daga cikin wadanda aka sace.
Ya ce ’yan sanda sun kara kaimi wajen gudanar da aikin “nema da ceto” tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai da mafarauta domin tabbatar da kubutar da sauran fasinjojin da ke hannun ’yan bindigar.
'Yan bindiga sun sace mutum 26 a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 26 bayan kashe wani bawan Allah a yankin karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi.
A ruwaito cewa 'yan bindigar sun saki mutane biyu daga cikin waɗanda suka sace; magidanci mai fama da rashin lafiya da wani mutum da ke da tabin hankali.
Mazauna yankin sun koka da yadda jami’an tsaro ba su kawo dauki ba, duk da cewa akwai ofisoshin 'yan sanda da na sojoji a ƙauyukan da ke kusa da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

