Tinubu zai Kawo Tsarin Aiki da ba a Taba Yi ba a Najeriya, Komai Zai Sauya a Ofisoshi
- Gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da shirin 1Gov domin sauya tsarin gudanar da aiki zuwa na zamani ba tare da amfani da takardu ba
- Shirin zai haɗa ma’aikatu da hukumomi a wuri guda ta hanyar amfani da fasahar zamani domin inganta aiki da rage ɓata lokaci
- Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa tsarin zai inganta tsaro, ya rage kashe kuɗi, tare da samar da gaskiya da gudanar da mulki cikin tsari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da fara aiwatar da cikakken shirin 1Gov kafin karshen shekarar 2025.
Shirin zai samar da dandali na musamman domin tabbatar da gwamnati na tafiya ba tare da amfani da takardu ba a ma’aikatu, hukumomi da sassa daban-daban.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan shirin ne a cikin wani sako da hadimin shugaba Bola Tinubu, Dada Olusegun ya wallafa a X.
Shirin yana ƙarƙashin jagorancin Galaxy Backbone kuma ma’aikatun gwamnati da dama sun fara shiga ciki.
Abubuwan da tsarin 1Gov ya ƙunsa
Shirin ya haɗa da kayan aiki na zamani da za su baiwa gwamnati damar gudanar da aiki cikin sauƙi da tsari.
A karkashin shirin akwai GovDrive domin adana takardu, GovMail a matsayin tsarin sadarwar gwamnati da GovE-Sign wanda zai maye gurbin sa hannu a takarda da na lantarki.
Haka kuma akwai GovConference domin tarurruka ta hanyar bidiyo, GovECMS don sarrafa ayyuka tsakanin ma’aikatu.
Tsarin zai kuma bayar da damar amfani da GovOTP domin tabbatar da tsaro da sahihancin bayanai a dukkan matakan aiki.
Magance ɓata lokaci da rashin gaskiya

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
Shugaban shirin, Wumi Oghoetuoma, ya bayyana cewa an kawo tsarin ne domin magance matsalar ɓata lokaci, tare da tabbatar da gaskiya a aikin gwamnati.
Ya ce shirin zai rage kashe kuɗi wajen buga takardu da adana su, sannan zai inganta gudanar da aiki cikin sauri da kuma tabbatar da cewa an rage cunkoson ayyuka a ofisoshin gwamnati.
Oghoetuoma ya kara da cewa wannan tsarin zai taimaka wajen saurin yanke shawara a tsakanin hukumomi, tare da tabbatar da cewa gwamnati tana gudanar da aiki cikin gaskiya da amana.

Source: Facebook
Za a dawo aiki da zamani a Najeriya
Shugaban Galaxy Backbone, Farfesa Ibrahim Adeyanju, ya bayyana kaddamar da shirin a matsayin sabon juyin juya hali a tafiyar gwamnati a Najeriya.
Nairametrics ta wallafa cewa ya ce shirin zai kawo canji wajen saurin yanke hukunci, tabbatar da tsaron bayanai, da kuma inganta hidima ga ’yan ƙasa.
Haka kuma wani jami’i daga ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ya bayyana cewa tsarin zai taimaka wajen inganta sadarwar diflomasiyya da hulɗar ƙasa da ƙasa.
Harajin gwamnati zai shafi 'yan Najeriya

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci
A wani rahoton, mun kawo muku cewa a shekarar 2026 ake sa ran cewa sabuwar dokar harajin Bola Tinubu za ta fara aiki.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa dokar za ta shafi ma'aikata, yan kasuwa da kusan dukkan 'yan Najeriya.
Wani bincike ya nuna cewa 'yan acaba, malaman makaranta, masu hawa motoci da jiragen sama za su fuskanci karin kudin da suke kashewa.
Asali: Legit.ng
