Bayan Shekaru 40, An Rufe Babban Masallacin Juma'an 'Yan Izala a Jihar Katsina
- Kungiyar Izala ta rufe babban masallacin Juma'a na garin Kankia a jihar Katsina sakamakon ambaliyar ruwa
- Masallacin ya shafe shekaru 40 ana sallah a cikinsa, kuma wannan ne karo na farko da ya fuskanci wannan kalubale
- Shugaban JIBWIS na Kankia, Alhaji Umaru Bature ya bayyana cewa sun fara shirin rusa masallacin domin gina sabo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Karamar Hukumar Kankia a Jihar Katsina, ta sanar da rufe Masallacin Juma’a da ke unguwar Layi.
Kungiyar JIBWIS da aka fi sani da Izala ta rufe masallacin wanda aka gina tun sama da shekaru 40 da suka wuce, sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye wurin.

Source: Original
Sheikh Khalil Kasim, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kankara, kamar yadda The Guardian ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa daga yanzu sallar Juma’a za a rika gudanar da ita a Masallacin Ibn Taymiyya da ke Gurara a nan cikin Kankia.
Izala ta rufe masallacin Juma'a a Katsina
Shehin malamin ya ce:
“Saboda ambaliyar ruwa da ta mamaye masallacin, mun dakatar da gudanar da salloli a cikinsa har sai komai ya wuce, za mu ba da sanarwa a lokacin da ya dace.”
Shugaban Izala na Kankia, Alhaji Umaru Bature, ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan taro da suka yi da Babban Limamin masallacin, Malam Tasiu Umar, da Shugaban Kwamitin Masallacin, Malam Alkhamis Rabiu.
Ya bayyana cewa an gina masallacin tun a shekarar 1985, amma kwararru sun ba da shawarar a rufe shi domin ambaliyar da ta shafi garin kwanan nan ta mamaye shi, cewar rahoton Gazette Nigeria.
Me yasa aka rufe masallacin 'yan Izala?
Bature ya kara da cewa:
“Mun rufe shi ne saboda haɗarin da ke tattare da yin sallah a ciki. Ginin na iya rushewa a kowane lokaci, ko yanzu ko bayan damina.
"Saboda haka ba wai sallar Juma’a kadai ba, har da sallolin yau da kullum mun dakatar da su. Mun kewaye masallacin muna shirin rusa shi domin a sake gina sabo.”

Source: Facebook
Izala ta fara neman taimakon gina sabon masallaci
Ya bukaci taimakon al’umma baki ɗaya da kamfanoni daga cikin gida da wajen ƙasar domin gina sabon masallacin.
“Muna maraba da duk wani tallafi a hanyar Allah. Mun riga mun sa an zana sabon gini ga wanda ke son taimaka mana wajen gina wani masallaci,” in ji shi.
Hukumar Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kwanan nan ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin Naira a Kankia.
Yadda shugaban Izala ya hadu da Inyass
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Izala na Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan ya ce ya hadu da Sheikh Ibrahim Inyass sau da dama a rayuwarsa.
Sheikh Yakubu Musa ya ce ya hadu da Sheikh Inyass fiye da sau daya a Najeriya, inda suka tattauna tare da gaisawa da juna.
Malamin ya ce da ya fada wa wani malamin darika irin yadda ya yi mu'amala da Inyass, ya fada masa cewa da a cikinsu yake da sai an rika zuwa neman tabarruki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


