'Dan Sanda Ya 'Bindige' Malami da Ya Je Yi Wa Gwamna Wa'azi har Gidansa
- Ana zargin gwamnati da sakaci wanda ya jawo hallaka wani matashi da ya yi kokarin yi wa gwamna wa'azi
- Wata uwa, ta zargi jami’an ‘yan sanda da kashe ɗanta, Moses, bayan ya nemi ya yi wa gwamnan Cross River wa’azi
- Victoria ta ce Moses ya je tsohon gidan gwamna don isar da saƙon Ubangiji, amma ‘yan sanda suka harbe shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Calabar, Cross River - Wata mata ta bukaci adalci game da kisan danta da 'yan sanda suka yi ba tare da dalili ba.
Ana zargin dan sanda ya hallaka matashin da ya je gidan gwamnan domin yi masa wa'azi da kira zuwa ga Ubangiji.

Source: Facebook
Uwa ta zargi 'yan sanda da hallaka danta
Rahoton Punch ya ce uwar matashin mai suna Moses Mba Onyekachi mai shekaru 23 ta bukaci adalci game da lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce abin ya faru ne a Calabar ranar 1 ga Agusta 2025, sun je jana’iza, sai suka samu kira da safe cewa a gaggauta zuwa asibitin sojojin ruwa saboda wata matsala.
Bayan mijinta ya isa wurin, sai ya gano ɗansu aka kai asibiti, suka ce ya nemi yin wa’azi a gidan gwamna Bassey Otu.
Moses ya bayyana cewa Ubangiji ne ya umarce shi ya kai saƙo, amma ‘yan sanda sun hana shi shiga sau biyu, daga ƙarshe sun ɗauki hakan a matsayin barazana.
Bayan haka aka ce an buge shi sannan aka harbe shi, ya kwanta cikin jini tun daga ƙarfe 11 na safe har zuwa bayan rana.

Source: Getty Images
Yadda matashin ya mutu a gadon asibiti
Jami’an Red Cross sun ji harbe-harbe da yamma, sun isa wurin suka tarar da shi cikin yanayi mai muni, aka garzaya da shi asibitin sojojin.
A asibitin an samu jinkiri, suka ce an ba shi kulawar gaggawa domin ya samu karfi da neman sama da N400,000 kafin tiyata.
Daga nan sai ciwon ciki mai tsanani da raunin bugun da ya sha suka karu, daga ƙarshe, ya mutu, Premium Times ta tattabar da labarin.
Mun kira wani jami’i, Emmanuel Dickson, wanda ya zo da wasu jami’an tsaro,, sai suka fara barin wurin nbayan an tabbatar ya mutu.
Ta ce a ranar Lahadi an kai gawarsa dakin ajiya, aka biya N54,000. Dickson ya yi alƙawarin taimako, amma abin da ya bayar kadan ne.
Har ila yau, ta ce washegari jami’an gwamnati da ‘yan sanda suka je wajen kwamishinan ‘yan sanda da kuma dakin ajiya ba tare da yardarsu ba, don duba gawar.
Ta ce akwai matsala saboda tun farko suna cewa ɗansu yana da tabin hankali, amma sun ki amincewa da haka.
Matashi ya hallaka mahaifiyarsa a Cross River
Kun ji cewa yan sanda sun kama Mathias Amunde bisa zargin kashe mahaifiyarsa da sanda a jihar Cross River.
An ce wanda ake zargin tare da wani abokinsa sun yi amfani da sanda wajen kashe tsohuwar, sannan suka jefa gawarta a rijiya.
’Yan sanda sun tabbatar da cewa za a ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma daukar mataki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

