Bayan Sanusi II Ya Gama Digirin PhD, Abba zai Jawo Jami'ar London zuwa Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya taya Sarki Muhammadu Sanusi II murna kan kammala digirin PhD a jami’ar SOAS ta London
- Ya bayyana shi a matsayin abin koyi ga al’umma tare da yabawa kan gudummawarsa a ilimi, tattalin arziki da sauran bangarori
- Gwamnan ya kuma sanar da shirin haɗin gwiwa da jami’ar London domin ƙarfafa jami'ar Northwest da ke jihar Kano a nan Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana farin ciki da taya murna ga Khalifa Muhammadu Sanusi II bisa nasarar kammala digirin PhD.
Rahotanni sun bayyana cewa Sarki Sanusi II ya kammala karatu ne a Jami’ar of London da ke Birtaniya.

Source: Facebook
A sakon da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook, gwamnan ya ce nasarar ta zama abin alfahari ga Najeriya baki ɗaya, la’akari da irin gudummawar Sarkin a fannonin rayuwa.

Kara karanta wannan
Masarautar Kano ta fitar da sako bayan Sarki Sanusi II ya gama digirin PhD a Landan
Abba Kabir ya bayyana shirin gwamnatin Kano na ƙulla alaƙar ilimi da Jami’ar London domin ƙarfafa jami'ar Northwest, ta yadda za ta kai matakin gogayya da manyan jami’o’i a duniya.
Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin abin koyi
A cikin sanarwar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana Sarkin Sanusi II a matsayin gwarzo, kwararre kuma abin koyi ga al’umma a yau da waɗanda ke tasowa.
Ya bayyana cewa digirin PhD ɗin da Sanusi ya samu wani sakamako ne na jajircewa da tsawon shekaru na jajircewa wajen ilimi, nazari da bada gudummawa ga ci gaban ƙasa.
The Guardian ta wallafa cewa gwamnan ya ce Sarkin ya kasance mutum mai kishin ilimi da sauya rayuwa ta hanyar adalci da kuma ba da shawarwari kan tattalin arziki da siyasa.
Abba ya fadi kokarin Sarkin Kano Sanusi II
Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa Sarkin na daga cikin manyan shugabannin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare al’umma.
Ya ce aikin Sanusi II na karantarwa da fafutuka wajen inganta tsarin tattalin arziki da zamantakewa, musamman a fannin ilimi, ya kasance haske ga 'yan Najeriya da ma duniya.
Ya yi addu’ar samun ƙarin hikima, lafiya da tsawon rai ga Sarkin domin Kano da Najeriya su ci gaba da amfana da iliminsa da ƙwarewarsa.
Hadin gwiwar Kano da jami’ar London
Baya ga taya murna, Gwamna Yusuf ya sanar da wani muhimmin shiri na haɗin gwiwa tsakanin Jihar Kano da Jami’ar London domin habaka jami'ar Northwest ta Kano.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa haɗin gwiwar za ta shafi batutuwan bincike, horar da malamai, da kuma ɗaukaka tsarin koyarwa bisa ƙa’idodin duniya.
Wannan, a cewarsa, zai bai wa jami’ar damar zama mai gogayya da manyan cibiyoyin ilimi a duniya.
An yi bikin yaye Sanusi II a London
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya halarci taron yaye dalibai da suka hada da Sanusi II a London.
A shekarar 2024 mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kammala digirin PhD a jami'ar London da ke Birtaniya.
Rahotanni sun nuna cewa kafin yaye daliban, Sarki Sanusi II ya jagoranci huduba da sallar Juma'a a wani asibiti a London.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
