Wasu Ma'aikata Sun Jawo Wa Kansu, Gwamna Ya Kore Su daga Aiki Nan Take
- Hukumar kula da ma'aikatan gwamnati a jihar Abia ta gano wasu da ke karbar kudaden da suka zarce albashinsu a wata
- Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya amince da korar wadannan ma'aikata tare da mika su ga hukumomin tsaro
- Ya kuma bayar da umarnin kara zurfafa bincike domin gano wadanda ake zargin sun taimaka masu a ofishin biyan albashi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Gwamnatin jihar Abia karkashin jagorancin Gwamna Alex Otti ta kori ma’aikata shida na Ma’aikatar Shari’a bayan gano suna da hannu a badakalar albashi.
Gwamnatin Abia ta ce bincike ya gano cewa ma'aikatan sun jirkita tsarin biyan albaalshi ta yadda ake tura masu makudan kudi da suka wuce hakkinsu.

Source: Facebook
Shugaban hukumar kula da harkokin ma'aikatan gwamnatin Abia, Eno Eze ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Sabuwar hukumar Kano ta zuba buri, tana shirin tarkato harajin N5bn kafin karshen 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen ma'aikatan da aka kora a Abia
Binciken ya gano cewa ma’aikatan sun yi amfani da dabara wajen juya tsarin biyan albashi, wanda ya ba su damar karɓar kuɗaɗen da suka wuce albashinsu na wata-wata.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da:
1. Mr. Dickson Uche Eze – Principal Accountant (SGL 12)
2. Mrs. Esther Emeruwa – Senior Accountant (SGL 10)
3. Mrs. Ijeoma Jonathan – Chief Executive Officer (Accounts – SGL 14)
4. Mrs. Treasure Isinguzo – Assistant Chief Executive Officer (Accounts – SGL 13)
5. Mrs. Chioma Victoria Erondu – Principal Executive Officer (Accounts – SGL 12)
6. Mrs. Hannah Ezinne Eze – Senior Executive Officer (General Duties – SGL 09)
Kwamitin hukumar ma’aikata ta jihar ne ya gudanar da bincike mai zurfi, inda aka gano cewa waɗannan ma’aikatan sun ci kudaden da ba na halal ba.
Sai dai kwamitin binciken ya wanke Mrs. Chioma Favour Madu, wadda ta gaggauta kai rahoto bayan ganin kudi fiye da albashinta.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
Gwamna Otti ya bada umarnin zurfafa bincike
Rahoton binciken ya kuma nuna yiwuwar akwai hannun wasu ma'aikatan ofishin biyan albashi a cikin wannan harkalla.
Gwamna Alex Otti ya bayar da umarnin gudanar da karin bincike domin tabbatar da gaskiya da gano duk masu hannu a wannan badakala.

Source: Facebook
Gwamna Otti ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mika waɗanda aka kora ga hukumomin tsaro domin fuskantar shari’a, rahoton Leadership.
A cewar gwamnatin jihar Abia, wannan mataki ya nuna aniyarta ta tabbatar da gaskiya, tsari, da kuma ba sani ba sabo game da batun cin hanci da rashawa.
Gwamna Otti zai dauki sababbin malamai 4000
Kuna da labarin, Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya bayyana shirinsa na daukar sababbin malamai 4,000 domin inganta harkokin neman ilimi.
Alex Otti ya ce manufar ita ce a samar da isassun malamai a makarantun jihar, ganin yawan ɗaliban da aka samu tun bayan aiwatar da tsarin ilimi kyauta.
Har ila yau, gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba za a tura malamai 5,394 da aka dauka aiki zuwa makarantu domin su fara aiki gadan-gadan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng