Fetur: Yadda Harajin Tinubu zai Shafi Ma'aikata, Masu Sana'a, 'Yan Kasuwa da Sauransu
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar harajin 5% a kan kayayyakin mai, wanda zai shafi fetur, dizal, da man jiragen sama
- Sabon tsarin zai shafi kowa daga 'yan acaba zuwa ‘yan kasuwa, malamai, dalibai da masu sana’o’i a fadin kasar nan
- A wannan rahoton, mun kawo muku bayan kan yadda harajin zai shafi rayuwar al'ummar Najeriya ta hanyoyi daban daban idan ya fara aiki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Sabuwar dokar harajin 5% da Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu a kanta za ta sauya tsarin kashe kudin mai ga ‘yan Najeriya da dama.
Wannan haraji dai zai shafi kayayyakin makamashi da suka hada da man fetur, dizal, man jirgin sama.

Source: UGC
Daily Trust ta wallafa cewa an ware kalanzir, gas din dafa abinci da kuma wasu makamashi daga tsarin, domin rage nauyi ga al’ummar kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma duk da wannan sassauci, ana ganin karin farashin da za a fara biyan nan gaba zai kara matsa wa iyalai da ‘yan kasuwa lamba a rayuwar yau da kullum.
Tasirin harajin ga ‘yan kasuwa/masu sana’a
Misali, a Kano, dan acaba da yake kashe N25,000 a mako kan man fetur zai rika bukatar N26,000 domin sayen mai.
Duk da yake karin N1,000 na iya zama kadan, idan aka tara shi mako-mako zai zama gibi babba wajen sayen kayan masarufi da kudin makaranta.
Haka kuma a Ibadan, 'yar kasuwa da ke cika janaretonta da N10,000 zai zama wajibi ta biya N10,500. A shekara daya, karin da hakan zai haifar zai iya tasiri a kasuwarta.
Masu sana’o’in hannu kamar walda ba su tsira ba, domin karin N500 a man N10,000 da suka saya zai iya zama cikas ga harkokinsu.
Tasirin harajin ga sauran 'yan Najeriya
Malaman makaranta da dalibai ma ba su tsira ba, misali a Ilorin, malamin da yake ware N50,000 a wata domin sufuri da bukatun gida zai rika kashe N52,500.
Karin da za a samu da zai iya kaiwa N30,000 a shekara kuma na iya biyan kudin kayan aiki a makaranta kamar littattafai ko abinci.

Source: Getty Images
Dalibin jami’a a Zariya da yake kashe N25,000 kan man fetur a wata, zai rika biyan N26,250. Karin N1,250 a kowane wata na iya hana shi siyan littafin karatu.
Ga masu motoci, karin ya fi muni. Wanda a Legas ke cika motarsa da N40,000 sau biyu a mako zai rika kashe N42,000. Karin N100,000 a shekara na iya biyan kudin inshora ko gyaran mota.
Alakar harajin da kudin hawa jirgin sama
Masu yawo a jiragen sama ma ba su tsira ba, domin man jirgin sama yana cikin kayayyakin da harajin ya shafa.
Tikitin jirgi daga Legas zuwa Abuja zai iya karuwa da N10,000 zuwa N14,000, wanda zai ninka kudin tafiya ga masu yawan zirga-zirga.
Ga ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da jama'a masu yawan hawa jirgi, karin na iya zama karami a farko, amma sannu a hankali zai iya haifar da babba gibi.
Harajin gwamnati na iya kara kudin man fetur

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya za su biya harajin N45 kan kowace litar fetur da suka saya daga 2026
A wani rahoton, kun ji cewa ana fargabar sabuwar dokar harajin Bola Tinubu da za ta fara aiki a 2026 za ta iya jawo karin kudin fetur.
Wani rahoto ya nuna cewa za a iya samun karin haraji a kudin litar mai da zai iya kaiwa N45 da zarar dokar ta fara aiki.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta ayyana rana ko watan da dokar za ta fara aiki ba har yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

