Attajirin Dan Kasuwa a Najeriya Ya Shiga Matsala, EFCC Ta Fara Nemansa Ruwa a Jallo

Attajirin Dan Kasuwa a Najeriya Ya Shiga Matsala, EFCC Ta Fara Nemansa Ruwa a Jallo

  • Hukumar EFCC ta ayyana neman shugaban kamfanin Sujimoto Luxury Construction Limited, Olasijibomi Suji Ogundele
  • Hakan ya biyo bayan zargin da EFCC take wa attajirin dan kasuwar na hannu a wasu harkallolin karkatar da dukiyar kasa
  • EFCC ta bayyana wuri na karshe da aka ga Ogundele, sannan ta roki duk mai sahihin bayani ya garzaya ofishin jami'an tsaro mafi kusa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Attajirin dan kasuwa dan asalin jihar Osun, Olasijibomi Suji Ogundele ya shiga jerin wadanda ake nema ruwa a jallo a Najeriya.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'adi (EFCC) ta ayyana neman Olasijibomi Suji Ogundele, ruwa jallo kan zargin aikata laifuffukan da suka shafi kudi.

Jami'an EFCC.
Hoton sanarwar EFCC da jami'an yaki da rashawa a bakin aiki Hoto: EFCC
Source: Facebook

EFCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa shafinta na Facebook yau Juma'a, 5 ga watan Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu

Ogundele dai shi ne shugaban kamfanin Sujimoto Luxury Construction Limited kuma ana yana daga cikin attajiran da suka mallaki biliyoyin Naira, in ji rahoton Leadership.

Me yasa EFCC ke neman attajirin?

A cikin sanarwar da ta fitar, hukumar EFCC ta ce tana neman Ogundele ne kan zargin “karkatar da kuɗi da kuma safarar kudin haram.”

EFCC ta bayyana cewa Ogundele, ɗan shekaru 44 daga ƙaramar hukumar Ori-Ade a jihar Osun, an gano cewa wurin da ya zauna na ƙarshe shi ne G29, Banana Island da ke Ikoyi a jihar Legas.

Sanarwar, wacce Dele Oyewale, Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na EFCC ya sanya wa hannu, ta ce:

“Mu na sanar da jama’a cewa hukumar yaki da masu yiwa tattaljn arzikin zagon kasa (EFCC) na neman Olasijibomi Suji Ogundele, wanda hotonsa ke sama, ruwa a jallo.
"Ana nemansa ne bisa zargin aikata laifin karkatar da dukiyar kasa da kuma safarar kudaden haram."

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya

Olasijibomi Suji Ogundele.
Hoton biliyoniyan dan kasuwa, Olasijibomi Suji Ogundele, wanda EFCC ke nema ruwa a jallo Hoto: Olasijibomi Suji Ogundele
Source: Facebook

EFCC ta fadi yadda za a kai mata bayanai

Hukumar EFCC ta roƙi duk wanda ke da sahihin bayani game da inda Ogundele ya buya da ya gaggauta kai rahoto ofishinta mafi kusa da shi.

“Duk wanda yake da bayanin da zai taimaka wajen gano inda yake, ya hanzarta tuntuɓar Ofishin EFCC mafi kusa da shi a Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, Fatakwal ko Abuja.
"Ko kuma ta tuntube mu ta wannan lambar waya: 08093322644; ko ta adireshin imel: info@efcc.gov.ng, ko ya garzaya ofishin ‘yan sanda ko hukumomin tsaro mafi kusa da ahi,” in ji EFCC.

EFCC ta ayyana neman tsohon kwamishinan Abia

A wani labarin, kun ji cewa EFCC ta ayyana tsohon kwamishinan kananan hukumomin Abia, Christopher Enweremadu, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

A sanarwar da EFCC ta fitar, ta ce ana zargin Enweremadu da hannu a cikin badakalar karkatar da kudin jama'a da kuma almundahana.

Hukumar EFCC ta roki duk wanda ke da masaniya a kan inda Enweremadu yake da ya tuntubi ɗaya daga cikin ofisoshinta da ke fadin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262