Sabuwar Hukumar Kano Ta Zuba Buri, Tana Shirin Tarkato Harajin N5bn kafin Karshen 2027
- Hukumar tallace-tallace ta Kano ta bayyana shirin da ta kunso ya tarkato wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf haraji mai yawa
- Shugaban hukumar, wacce gwamna ya kafa a 2025, Kabiru Dakata ya ce kafin karshen 2025 kadai, hukumar na sa ran samo N1.5bn
- Ya kuma bayyana yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya samo hikimar kirkirar hukumarsa, da yadda za ta gudanar da aiki a jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar da ke kula da sanya tallace-tallace da kula da alluna ta jihar Kano ta bayyana cewa tana da burin tara kudin shiga har N5bn kafin ƙarshen shekarar 2027.
Shugaban sabuwar hukumar, Kabiru Dakata, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai da aka gudanar a birnin Kano a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Kano: An sake tono badakalar biliyoyi da ta shafi jami'in Abba da Gwamna yake Landan

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Dakata ya ce hukumar ta fara da burin tara Naira biliyan 1.5 kafin ƙarshen shekarar 2025, sannan za ta ƙara azama a shekarar 2026 domin tara akalla N3bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar Kano na shirin tara harajin N1.5bn
Jaridar Solacebase ta wallafa cewa Kabiru Dakata ya tabbatar da kudirin sabuwar hukumarsa na sama wa gwamnatin Kano kudin shiga a 2025.
Dakata ya bayyana cewa:
"Burinmu shi ne tara N1.5bn cikin watannin da suka rage na 2025. A 2026 muna sa ran samun N3bn, sannan daga nan zuwa ƙarshen 2027, za mu kai ga tara N5bn in sha Allah."
Ya ce an kafa hukumar ne domin tsaftace harkar tallace-tallace a jihar, tare da hana maimaitawa da takurawa da masu karɓar haraji ke yi a jihar.
Ya ce:
“Tun bayan kafa wannan hukuma, ba wani haraji daban-daban ake karɓa daga masu tallace-tallace. Ita kadai ce hukumar da aka dora wa alhakin hakan.”

Kara karanta wannan
Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu
Kano: Hukumar tallace tallace ta samma aiki
Dakata ya ƙara da cewa dokar kafa hukumar ta samo asali ne daga irin misalan da aka gani a jihohin Legas, Ribas da Neja, inda aka samu irin wannan hukuma mai tabbatar da bin doka.
Ya ce an tanadi hukunci mai tsauri ga masu karya doka da suka haɗa da daurin wata ɗaya a gidan gyaran hali, aikin al'umma na tsawon watanni, ko kuma biyan tara daga N100,000 zuwa N500,000.

Source: Facebook
Ya ce:
“Za mu yi aiki da sauran hukumomin tallace-tallace domin kauce wa yin amfani da kalmomin batsa ko waɗanda ke cutar da martabar al’umma a cikin tallace-tallace.”
Ya ce lissafin kudin haraji na tallace-tallace ya danganta da girman allon tallan, wurin da aka kafa shi, da kuma adadinsa a jihar.
An kuma bankado badakala a Kano
A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta musanta zargin da wasu kungiyoyin farar hula suka yi mata na hana su gudanar da wata zanga-zangar lumana da suka shirya.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
Zanga-zangar dai na da nufin tursasa hukumomi su gurfanar da wani hadimin Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ake zargi da karkatar da makudan kudin gwamnati.
Ana zargin Abdullahi Ibrahim Rogo, wanda shi ne Darakta Janar na harkokin kula da fadar gwamnatin da karkatar da kudade har Naira biliyan 6.5 daga baitul mali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng