Masarautar Kano Ta Fitar da Sako bayan Sarki Sanusi II Ya Gama Digirin PhD a Landan
- Jami'ar SOAS da ke birnin Landan ta shirya yaye Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II bayan kammala digiri na uku
- Masarautar Kano ta fitar da sakon taya murna ga Mai Martaba Sarki Sanusi II bisa wannan nasara da ya samu a rayuwarsa
- Tuni dai tawagar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ta isa Landan domin halartar bikin yaye Sanusi II wanda ya karbi shaidar digirin digirgir
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Majalisar Masarautar Kano ta bayyana jin daɗi da alfahari bisa kammala karatu da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya yi.
Masarautar ta taya Sarki Sanusi II murna bisa kammala karatun digiri na uku "Doctor of Philosophy (PhD)" a fannin Shari’a, a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Source: Twitter
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da masarautar Kano ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya isa London domin bikin yaye Sarki Sanusi II bayan gama digiri na 3
Muhammadu Sanusi II ya kammala digirin PhD
Muhammadu Sanusi II ya kammala digiri na uku ne a shahararriyar Jami’ar Landan, School of Oriental and African Studies (SOAS).
A cewar sanarwar, wannan babban nasara ce da ta zamo tarihi ga masarautar Kano, mutanen Kano da kuma Najeriya baki ɗaya.
Sanusi II ya dade yana da neman ilimi tun kafin hawansa kan kujerar sarauta a jihar Kano, a shekarar 1981 ya kammala digiri na farko a fannin tattalin arziki.
A 1997, Muhammadu Sanusi ya kammala karatun digiri na biyu a fannin Fikihun Musulunci a wata jami'a da ke Khartoum, Sudan.
Bayan tsige shi daga matsayin Sarkin Kano na 15 a 2020, Sanusi II ya koma jami’ar SOAS da ke London domin ci gaba da karatu.
A shekarar 2024, Sanusi II ya kammala karatun digiri na uku a Landan a fannin shari'a, wanda a wannan makon jami'ar SOAS ta shirya yaye basaraken.
Masarautar Kano ta taya Mai martaba murna
Masarautar Kano ta bayyana Sanusi II a matsayin shugaba mai hangen nesa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen neman ilmi, gyaran al’umma da kare muradun jama’a.
Ta ce hakan ya kara tabbatar da ahi a matsayin ɗaya daga cikin manyan shugabannin Afirka da ke da tasiri a fannoni daban-daban na rayuwa, musamman ilimi, tattalin arziki da shugabanci.

Source: Twitter
Haka kuma, Majalisar Masarautar Kano ta yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki (SWT) ya ci gaba da ba wa Sarki Sanusi II lafiya, jagoranci nagari, da cikar buri wajen hidima ga al’umma da kuma ci gaban Najeriya.
Sanarwar ta ce:
"Majalisar Masarautar Kano ta taya Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, CON, murnar samun digirin PhD daga Jami’ar SOAS, Landan.
"Wannan babban lokaci ne na alfahari da ya nuna jajircewarsa tsawon rayuwa wajen neman ilimi, shugabanci, da hidima ga al'umma."
Gwamna Abba ya tafi bikin yaye Sanusi II
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu manya sun tafi Landan domin halartar bikin yaye Sarki Muhammadu Sanusi II a jami'ar SOAS.
Jami'ar SOAS da ke kasar Birtaniya ta shirya yaye Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi bayan ya kammala karatun digiri na uku.
Ana sa ran basaraken zai jagoranci Sallar Juma'a yau 5 ga watan Satumba, 2025 a Masallacin New Peckham, London.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

