Badaƙalar N6.8bn: Ƴan Sanda Sun Yi Martani kan Haramta wa Kungiyoyin Zanga Zanga a Kano
- Jami'an tsaro a Kano sun haramta wa kungiyoyin fararen hula gudanar da zanga-zanga a jihar
- Kungiyoyin sun shirya yin zanga-zanga a kan zargin badakalar Naira biliyan 6.5 a gwamnatin Abba Kabir Yusuf
- Amma rundunar ta ce ba zanga zanga ta hana ba, illa ɗaukar ƙwararan matakan tsaro zaman lafiya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta musanta zargin da aka yi mata na hana ƙungiyoyin fararen hula gudanar da zanga-zangar lumana a jihar.
Kungiyoyin sun kudiri aniyar yin zanga-zanga domin kira da a gurfanar da wani hadimin gwamnan Kano a gaban kotu.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa ana zargin Abdullahi Ibrahim Rogo da karkatar da Naira biliyan 6.5 daga asusun jihar.

Kara karanta wannan
Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun musanta zargin hana zanga-zanga
Daily Post ta ruwaito cewa Mai magana da yawun rundunar, SP Haruna Kiyawa, ya ce ba su hana matasan gudanar da zanga-zanga ba.
Ya ce:
“Babu wani sabon shingen tsaro da aka kafa, abin da aka gani aikin tsaro ne na yau da kullum da rundunar ‘yan sanda ke yi a cikin birni.”
Sai dai kuma, kungiyoyin fararen hula guda bakwai sun gudanar da taron manema labarai a Kano a ranar Alhamis a kan batun.
Sun bukaci buƙaci hukumomin EFCC da ICPC da su jajirce wajen ganin an tabbatar da adalci a kan zargin.
Kungiyoyin sun yi taro a jihar Kano
Shugaban Arewa Initiative of Sustainable Development and Humanitarian, Abdullahi Muhammad ne ya yi magana a madadin kungiyoyin.
A cikin jawabinsa, ya yi zargin cewa wasu mutane na ci gaba da karkatar da makudan kudi daga baitul-mali.

Source: Facebook
Ya ce:

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
“An ci amanar jama’a, an karkatar da biliyoyi, mutane na ci gaba da wahala yayin da wasu kalilan ke ƙara arzuta kansu."
Ya kuma lissafa wasu badakalolu da ke gaban gwamnatin jihar domin tabbatar da an bibiye su.
Daga cikinsu akwai badakalar magungunan Novomed, badakalar kwangilar ACRESAL, shirin tallafin kudi Naira 50,000 ga mata, da kuma ayyukan manyan titunan Kano.
Kungiyoyin sun kuma bukaci gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bincike kan badakalar Naira biliyan 6.5 tare da daukar mataki kan wadanda aka samu da laifi.
Sun bukaci bangaren shari’a ya tsaya a kan gaskiya ba tare da son zuciya ko amincewa da cin hanci ba, domin kauce wa yanke hukuncin da zai saɓa da gaskiya.
Hadimin Gwamnan Kano ya tafi kotu
A baya, mun wallafa cewa Babbar kotun majistare a Kano, ƙarƙashin Alkali Abdulaziz M. Habib, ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan Jafar Jafar.
Wannan umarni ya fito ne bayan ƙarar da Daraktan Kula da Harkokin Gidan Gwamnatin Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya shigar a kan Ja'afar Ja’afar da Audu Umar.
A cewar Rogo, wallafe-wallafen da aka yi a ranakun 22 da 25 ga watan Agusta, 2025, a jaridar Daily Nigerian mallakin Jafar Jafar sun ci mutuncinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng