Ranar Juma'a: Ruwan Sama da Iska Mai Karfi Zai Sauka a Kano da Jihohin Arewa 17
- NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama da iska mai karfi hade da tsawa a Kudu da Arewacin Najeriya, a yau Juma’a
- Hukumar ta ce iska mai karfi da tsawa na iya kawo matsalar zirga-zirga, daukewar wuta ko kuma ambaliya a wasu yankuna
- Yayin da aka shawarci jama'a su kasance cikin shiri, NiMet ta ce jihohi 30 da ruwan zai sauka sun hada da Kano, Bauchi da Kogi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar da cewa za a samu ruwan sama mai karfi a jihohi da dama na kasar nan a ranar Juma'a.
Hukumar ta ce ruwan da iska mai karfi, na iya kawo tsaiko a harkokin yau da kullum, musamman zirga-zirga da kasuwanci.

Source: UGC
Hasashen ruwan sama a Arewa
NiMet ta fitar da rahoton hasashen yanayin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a daren ranar Alhamis, 4 ga Satumba, 2025.
A cewar sanarwar, ana sa ran iska mai karfi za ta taso, sannan ruwan sama da tsawa su biyo baya a safiyar Juma’a a jihohi kamar Taraba, Jigawa, da Gombe.
Sauran jihohin da za su fuskanci ruwan sama a safiyar Juma'ar sun hada da Bauchi, Kebbi, Sokoto, Zamfara, Kano, Kaduna da Katsina.
A yammacin Juma'a kuwa, rahoton ya ce ruwan sama mai matsakaicin karfi zai sauka a Sokoto, Katsina, Kano, Zamfara, Kebbi, Kaduna, Taraba, Borno da Adamawa.
Hasashen ruwan sama a Arewa ta Tsakiya
NiMet ta ce a safiyar Juma'a, jihohin Filato da Benue za su fuskanci ruwan sama mai hade da iska mai karfi, da kuma tsawa.
Sai dai daga yammaci zuwa dare, za a tsumayi saukar ruwan sama a wasu sassan Nasarawa, Benue, Neja, Filato, Kogi, Kwara da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
'Za a yi kwanaki 5 ana malala ruwa,' Gwamnati ta jero jihohi 14 da za su gamu da ambaliya
Hasashen ruwan sama a jihohin Kudu
A shiyyar Kudancin Najeriya, NiMet ta ce akwai yiwuwar saukar ruwan sama kadan a safiyar Juma’a, musamman a jihar Cross River.
Amma daga yammaci zuwa dare, za a samu ruwan sama mai yawa a sassa da dama ciki har da Enugu, Ebonyi, Imo, Anambra, Abia, Edo, Delta, Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Bayelsa.

Source: Getty Images
Shawarwarin NiMet ga jama’a
Hukumar ta shawarci jama’a da su yi taka tsantsan yayin da ruwan sama ke sauka, inda ta ce iska mai karfi na iya rage ganin direbobi, wanda zai iya haddasa hadurra.
NiMet ta kuma gargadi al’umma da ke zaune a wuraren da ke bakin teku, ko ke yawan fuskantar ambaliya da su kasance cikin shiri saboda yiwuwar ambaliyar.
Taraba: Garuruwa 7 sun nutse a cikin ruwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, akalla garuruwa bakwai ne suka nutse a cikin ruwa a karamar hukumar Lau da ke jihar Taraba, sakamakon ambaliya.
Majiyoyi sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta jawo rushewar gidaje, lalacewar gonaki da kuma mutuwar daruruwan dabbobi a wadannan garuruwa.
Gwamnatin jihar Taraba ta bayyana cewa ta tura tawagar taimako domin ceto wadanda suka makale a gidajensu bayan ambaliyar, da kuma sama masu matsugunni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

