An Samu Aukuwar Mummunar Ambaliya a Taraba, Kauyuka 7 Sun Nutse a cikin Ruwa

An Samu Aukuwar Mummunar Ambaliya a Taraba, Kauyuka 7 Sun Nutse a cikin Ruwa

  • An samu afkuwar mummunar ambaliyar ruwa a jihar Taraba, wacce ta jawo asarar rayuka da haddasa barna a garuruwa bakwai
  • Garin Kunini ne ambaliyar ruwan ta fi shafa a karamar hukumar Lau, inda ta rusa gidaje, ta lalata gonaki kuma ta hallaka dabbobi
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya, ta yi hasashen cewa Gombe, Neja, Kogi da wasu jihohi za su fuskanci ambaliya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba - Mummunar ambaliya ta sake mamaye wasu garuruwa a jihar Taraba, bayan saukar mamakon ruwan sama da iska mai karfi.

Rahotanni sun nuna cewa garin Kunini ne ya fi fuskantar barna a cikin garuruwa bakwai da suka nutse a cikin ruwa bayan afkuwar ambaliyar a karamar hukumar Lau.

Ambaliyar ruwa ta yi barna a garuruwa bakwai na jihar Taraba
Gidaje sun nutse a cikin ruwa yayin da aka samu mummunar ambaliya a Borno, 2024. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

Garuruwa 7 sun nutse a ruwa a Taraba

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

Jaridar Daily Trust ta gano cewa gidaje da gonaki da dama sun nutse a ruwan, lamarin da ya tilasta daruruwan mazauna yankin barin muhallansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Julius, kwamishinan ci gaban karkara da birane a Taraba, wanda shi ma dan yankin ne, ya bayyana cewa ba su taba ganin irin wannan ambaliya ba.

Ya ce an yi asarar daruruwan dabbobi da dukiya mai yawa, yayin da ya tabbatar da cewa hukumomi sun fara aikin kwashe mata da yara daga gidajen da ruwa ya mamaye.

Peter Julius ya kara da cewa gwamnati za ta hanzarta samar da matsuguni na wucin gadi domin kada ambaliyar ta haifar da karin matsaloli ga wadanda abin ya shafa.

Ambaliya: Halin da mazauna Taraba ke ciki

Yohana Kwana, wani shugaba a garin Kunini, ya ce ambaliyar ta girgiza su matuka saboda irin asarar da suka yi a wannan karo.

Ya bayyana cewa al’ummarsu ba ta taba fuskantar irin wannan bala’i ba, inda gonaki, ababen more rayuwa da dabbobi suka salwanta cikin kankanin lokaci.

Yohana Kwana ya kuma yaba wa gwamnati bisa kokarin da take yi na kai daukin gaggawa ga mutanensu da wannan ambaliya ta shafa.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun cimma matsaya kan rashin tsaro, sun sanar da Shugaba Tinubu

NEMA, SEMA sun dauki matakai kan ambaliya

An gano cewa ma’aikatar muhalli ta Taraba ta taba yin gargadi ga mazauna bakin kogin Benue da su koma wurare mafi aminci saboda hatsarin ambaliya.

Gwamnati ta tura jami'ai domin ceto wadanda ambaliya ta rutsa da su a Taraba
Jami'ai na kokarin ceto wadanda ambaliya ta rutsa da su a Maiduguri, jihar Borno a 2024. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai, an ce da yawa daga cikin mazauna garuruwan bakin kogin, sun ki daukar shawarar gwamnati, inda suka ci gaba da zama har mai afkuwa ta afku.

Duk da haka, wata sanarwa daga shafin hukumar NEMA na X, ta nuna cewa hukumar SEMA a Taraba ta kwashe wasu mazauna kananan hukumomin Lau da Jalingo zuwa wuri mai aminci.

Sanarwar ta ce akalla mazauna gidaje 207 ne daga garuruwa bakwai na karamar hukumar Lau ne aka sauya wa matsugunni.

Sai dai duk da wannan kokari, za a iya cewa, garuruwa bakwai sun shiga kangin wahala bayan afkuwar sabuwar ambaliyar ruwan a karamar hukumar Lau.

Ambaliya za ta shafi jihohi 29 a Satumba

Tun da fari, mun ruwaito cewa, ana fargabar ambaliyar ruwa za ta shafi babban birnin tarayya Abuja da jihohi 29 daga 1 zuwa 15 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kawo shirin NASAP domin koya wa matasa 100,000 ayyuka

Gwamnatin tarayya ta fitar da rahoton gargadin ambaliya, inda ta ce kananan hukumomi 107 da garuruwa 631 ne ke fuskantar barazanar ambaliyar.

Ta bakin hukumar NiHSA, gwamnati ta ce jihohin da ambaliyar za ta iya shafa sun hada da Adamawa, Anambra, Bauchi da Kogi, dai sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com