Girma Ya Karu: Za a Karrama Sheikh Daurawa da Digirin Dakta a Jami'ar Danfodio

Girma Ya Karu: Za a Karrama Sheikh Daurawa da Digirin Dakta a Jami'ar Danfodio

  • Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta sanar da karrama Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Dakta saboda hidimarsa ga ilimi da al’umma
  • Bikin zai gudana ne ranar Asabar mai zuwa a Sokoto, tare da shagalin cikar jami’ar shekara 50 da yaye ɗaliban da suka kammala karatu
  • Sheikh Daurawa zai jagoranci sallar Juma’a a Masallacin Farfesa A. A. Gwandu yayin da sauran malamai za su yi a wasu manyan masallatai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sokoto – Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta bayyana cewa za ta bai wa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Dakta a wani babban biki da za a gudanar a birnin Sokoto.

Karramawar na zuwa ne sakamakon gudumawar Sheikh Daurawa wajen yada ilimi da kuma ayyukan wa’azi da ya dade yana yi a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sowore, Jafar Jafar, Hamdiyya da wasu 'yan gwagwarmayar da aka kai kotu

Sheikh Daurawa yana wa'azi a wani masallaci
Sheikh Daurawa yana wa'azi a wani masallaci. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Malamin addinin Musulunci, Farfesa Mansur Sokoto ne ya fitar sanarwar a wani sako da ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bikin karramawar zai kasance cikin manyan tarukan da suka shafi cikar jami’ar shekara 50 tun bayan kafuwarta.

Jami'ar Ɗanfodiyo za ta ba Sheikh Daurawa Dakta

Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto ne za ta karrama Sheikh Daurawa da wajen ba shi Dakta a wani ɓangare na cikar jami’ar shekara 50.

A cewar Farfesa Mansur Sokoto, Sheikh Daurawa ya cancanci haka saboda irin gudumawar da ya bayar wajen ilimi da wa’azi a cikin al’umma.

Shirye-shiryen sallar Juma’a da wa’azi

A yayin da ake shirye-shiryen babban bikin, Sheikh Daurawa zai jagoranci sallar Juma’a a Masallacin Farfesa A. A. Gwandu.

Sheikh Dr. Nazif Inuwa zai yi huduba a Masallacin Abu Huraira (RA), yayin da Sheikh Dr Mujahid Aminuddin zai yi a Masallacin Anas bn Malik.

Malamai ukun za su haɗu domin gudanar da wa’azin dare a Masallacin Abu Huraira (RA) bayan sallar Magrib har zuwa Isha’i, a madadin karatun Sahihul Bukhari da ake gudanarwa a lokacin.

Kara karanta wannan

Izala za ta hada Tinubu, El Rufa'i da manyan kasa a taron da za ta yi a Kaduna

Waye Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa?

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa fitaccen malamin addinin Musulunci ne da ya fito daga jihar Kano.

A shekarar 2023, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada shi a matsayin shugaban Hisbah na jihar, bayan ya taba rike wannan mukami a gwamnatocin baya.

Daily Trust ta rahoto cewa a 2024 malamin ya yi murabus daga matsayin amma ya dawo bayan an yi sulhu.

Sheikh Daurawa yayin da ya ke tafsiri a jihar Gombe
Sheikh Daurawa yayin da ya ke tafsiri a jihar Gombe. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Sheikh Daurawa ya shahara wajen tafsirin Alƙur’ani mai girma a lokacin watan Ramadan, musamman a birnin Gombe inda ya shafe kimanin shekaru 20 yana gudanar da tafsiri.

An kafa dokar wa'azi a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta kafa dokar wa'azi da ta shafi malaman Musulunci da Kirista.

Shugaban hukumar kula da harkokin addini a jihar ya ce an ba dukkan masu wa'azi wata biyu su yi rajista domin a tantance su.

Sai dai lamarin bai yi wa wasu malamai dadi ba kuma sun bukaci gwamnatin jihar da ta sake nazari kan dokar da ta kawo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng