'Yan Sanda Sun Gayyaci El Rufai da Wasu Ƴan Siyasa 6 kan abin da Ya Faru a Kaduna
- Rundunar ’yan sanda ta gayyaci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC a jihar
- An gayyace su ne kan zargin hada baki, tada zaune-tsaye, ɓarnatar da dukiya da kuma jikkata mutane a wani taron siyasa
- Nasir El-Rufai ya yi martani ga 'yan sanda kan abin da ya faru a Kaduna yayin da jigon ADC ya magantu kan takardar gayyatar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Rundunar ‘yan sandan Kaduna, ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC domin amsa tambayoyi.
A cewar wata wasika da Legit Hausa ta gani, an gayyaci El-Rufai ne bisa zargin hada baki, da tayar da tarzoma, da kuma raunata mutane.

Source: Facebook
Kaduna: 'Yan sanda sun gayyaci El-Rufai
Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, mai kula da sashen binciken manyan laifuffuka (CID), Uzainu Abdullahi ne ya sanya wa takardar hannu, a ranar 4 ga Satumba, 2025, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen wadanda ake gayyata, da aka ambata a cikin takardar sun hada da:
- Malam Nasir El-Rufai
- Bashir Sa’idu
- Jafaru Sani
- Ubaidullah Mohammed (30)
- Nasiru Maikano
- Aminu Abita
- Ahmed Rufa’i Hussaini (Mikiya)
Sanarwar da aka aike wa shugaban jam'iyyar ADC na Kaduna, ta ce:
"An buƙace ka, ka kawo wadanda aka ambata zuwa sashin SCID domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da masu ƙarar suka kawo a kansu a ranar 8 ga Satumba, 2025."
Martanin jam’iyyar ADC a Kaduna
Jafaru Sani, mataimakin shugaban ADC na Arewa maso Yamma, wanda sunansa ya fito cikin jerin wadanda ake gayyata, ya ce mafi yawansu sun samu labarin gayyatar ne ta shafukan sada zumunta.
A zantawarsa da jaridar Daily Trust, Jafaru Sani, ya ce ba zai iya yin karin bayani game da gayyatar ba tukunna.
Sabani tsakanin gwamnati da El-Rufai
A makon da ya gabata, gwamnatin Kaduna da El-Rufai sun yi musayar maganganu kan tashin hankali da ya faru a wani taron ADC da aka shirya a jihar.
Gwamnatin Kaduna ta zargi tsohon gwamnan da kokarin tayar da rikici da jawo rarrabuwar kawuna a jihar, zargin da ya El-Rufai ya musanta.
Mun ruwaito cewa, Dr. Suleiman Shuaibu, kwamishinan tsaro na jihar, ya ce gwamnati ba za ta zuba ido ta kyale tsohon gwamnan da ya bar jihar a ruɗani ya jefa ta cikin wani sabon rikici ba.

Source: Twitter
Nasir El-Rufai ya kare kansa
A martanin da ya yi, El-Rufai ya ce gwamnatin Uba Sani na kokarin kulle bakin 'yan adawa ta hanyar zarge-zargen da ba su da tushe.
Ya ce jam’iyya mai mulki na amfani da rikicin da ya faru a taron ADC a matsayin hujjar hana adawa yin tasiri a jihar.
El-Rufai ya soki 'yan sandan Kaduna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Nasir El-Rufai ya bayyana matuƙar rashin jin daɗinsa kan umarnin ‘yan sanda na hana taron shugabannin ADC a Kaduna.
Tsohon gwamnan jihar na Kaduna ya ce abin da 'yan sandan suka yi ya saba da tanade-tanaden kundin tsarin mulki na Najeriya.
El-Rufai ya zargi kwamishinan ‘yan sandan Kaduna da karbo umarnin kotu da ya hana taron ba tare da an bin hanyoyin da suka dace ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

