Al'umma Sun Samu Sauƙi, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Rikakken Ɗan Ta'adda da Yaransa 4

Al'umma Sun Samu Sauƙi, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Rikakken Ɗan Ta'adda da Yaransa 4

  • Yan bindiga na ci gaba da hallaka junansu musamman a yankin Arewacin Najeriya yayin da sojoji ke nakasa su a daya gefen
  • Jagoran yan ta'adda, Kachalla Abu Dan Barka, da wasu mayaƙansa sun mutu a harin abokan gaba a karamar hukumar Maru, Zamfara
  • An ce an kashe Dan Barka ne da mayaƙansa lokacin da aka yi musu kwanton-bauna a yankin Dansadau

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zamfara - Majoyoyi sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun gwabza da juna inda aka yi rashin mayaka da yawa.

An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a wani yanki da ke karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

Yan bindiga sun yi wa junansu illa a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Zagazola Makama ya ce fitaccen dan bindiga, Kachalla Abu Dan Barka, tare da mayaƙansa huɗu, sun mutu.

Kara karanta wannan

Gaba ta yi tsanani tsakanin yan bindiga, an kashe wasu jagorori 2 da suka addabi jama'a

Yadda yan bindiga ke hallaka junansu

Wannan ba shi ne karon farko ba da yan bindiga ke hallaka junansu wanda ke rage wa sojoji kokarin kakkabe su a kullum.

Ko a yau an ruwaito cewa wasu yan bindiga suka yi wa manyan hatsabiban 'yan ta'adda kofar rago a jihar Zamfara.

Rahoto ya nuna cewa an kashe jagororin dabar yan bindiga biyu, Kachalla Bingil da Kachalla Mai Hidima a yankin karamar hukumar Maru.

Wasu majiyoyi sun bayyana yadda hatsabiban yan ta'addan suka gamu da ajali lokacin da suka fito rangadi a kauyukan yankin.

Hatsabibin dan bindiga da yaransa sun mutu

An ce lamarin ya faru ne a gabashin kauyen Magana Mai Rake, kusa da Yar Tashar Sahabi a yankin Dansadau.

Majiyoyi sun ce an yi musu kwanton bauna ne yayin da suke wucewa ta yankin, inda suka gamu da kisan kai ba zato.

“Kachalla Abu Dan Barka sanannen kwamanda ne da ke sheke ayarsa a yankin Dansadau.

Kara karanta wannan

Ado Aleiro: Jagoran 'yan bindiga ya kashe mayakansa a Zamfara, an ji dalili

"Ana shirya hare-hare a matsuguninsa a kauyen Madada da satar shanu da garkuwa da mutane a Maru da sauran kananan hukumomi.

- Cewar wata majiya

Yan ta'adda sun kashe wani jagoran yan bindiga a Zamfara
Gungun yan bindiga da dakarun sojoji a Najeriya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Zamfara: Matsalolin da yan bindiga ke fuskanta

Kisan Dan Barka na nuna ƙara tsanantar rikici tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Zamfara, inda hare-hare da rikice-rikicen cikin gida suka ƙaru.

An bayyana cewa yankin Dansadau, wanda aka dade ana ɗauka a matsayin sansanin manyan 'yan ta’adda, ya shiga rikice-rikice tsakanin kungiyoyi.

Duk da ƙoƙarin jami’an tsaro a Zamfara da Arewa maso Yamma, ‘yan bindiga suna fuskantar barazana daga rikice-rikicen cikin gida da cin amanar juna.

Majiya ta bayyana cewa ana ci gaba da bibiyar karuwar yaƙe-yaƙen cikin gida tsakanin kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin.

Ado Aliero ya hallaka mayakansa a Zamfara

Mun ba ku labarin cewa rigima ta kunno kai a sansanin tantirin jagoran 'yan bindiga, Ado Aleiro, wanda yake ta'addancinsa a Zamfara da wasu jihohi.

Hatsabibin dan bindigan ya bindige wasu daga cikin mayakansa bayan zargi ya shiga tsakaninsa da su.

Ado Aleiro ya dade da shiga cikin jerin 'yan ta'addan da hukumomi suke nema saboda yadda yake gudanar da ayyukan ta'addancinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.