'Da Gaske ne,' 'Yan bindiga Sun Yi Garkuwa da Sarki Mai Daraja Ta 2 a Jihar Kogi
- ’Yan sanda sun tabbatar da cewa an sace sarki mai daraja ta biyu, kuma Hakimin Bagaji Ado a karamar hukumar Omala, jihar Kogi
- Rundunar ta ce 'yan bindiga sun kai wa basaraken hari ne yayin da yake dawowa daga taron majalisar sarakuna a Abejukolo
- An bayyana matakan da 'yan sanda, sojoji, mafarauta da ’yan sa-kai suka dauka don ceto basaraken daga hannun masu garkuwar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Lokoja - Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun sace basarake mai daraja ta biyu a masarautar Bagaji Odo, da ke a karamar Hukumar Omala.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Williams Ovye-Aya ne ya tabbatar da sace basaraken a wata hira da ya yi da manema labarai a Lokoja.

Source: Twitter
'An sace Sarki David Wada' - 'Yan sanda
A tattaunawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), Williams Ovye-Aya ya ce ofishin 'yan sanda na Omala ya samu kiran gaggawa kan sace basaraken a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wani ne ya kira 'yan sanda, sace wasu 'yan bindiga sun tare ayarin motoci, sun sace Mai martaba Sarki David Wada, wanda basarake ne mai daraja ta biyu a masarautar Bagaji Odo, kuma hakimin Bagaji Odo.
Ovye-Aya ya ce 'yan bindiga sun sace Sarki Wada ne lokacin da yake dawowa daga wani taron majalisar sarakuna a Abejukolo, hedikwatar karamar hukumar Omala.
A cewar kakakin 'yan sandan, 'yan bindigar sun yi kwanton bauna a dai-dai garin Ojuwo Ugweche, inda aka sace basaraken zuwa cikin daji.
Kokarin da ake yi na ceto sarki a Kogi
Williams Ovye-Aya ya ce:
“Mun gaggauta kai dauki bayn samun kiran gaggawa ta hanyar tura tawagar yaki da masu garkuwa da mutane da hadin gwiwar 'yan banga, inda suka shiga daji don ceto basaraken daga hannun wadanda suka sace shi.
"Yanzu haka da muke magana da ku, jami'an tsaro suna sintiri a cikin daji domin gano 'yan bindigar da kuma ceto basaraken cikin koshin lafiya."
Jaridar This Day ta rahoto sarki mai daraja ta daya a Omala, Onu Ife, Boniface Musa, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da ceto Sarki Wada.

Source: Original
Girke jami'an tsaro bai hana ta'addanci ba
Sace basaraken na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ta tura sojoji da sauran jami'an tsaro zuwa karamar hukumar, lamarin da ake ganin bai hana karuwar rashin tsaro da sauran laifuffuka ba.
Jaridar Punch ta tuno cewa, bayan mummunan hare-hare da kona gidaje a garuruwa Bagana, Bagaji, Agojeju Odo, da Ajokpachi Odo da 'yan bindiga suka yi a shekarar 2024, Gwamnatin Tarayya ta tura dakaru da sauran jami'an tsaro zuwa yankin don dawo da zaman lafiya.
Amma abin takaici, 'yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare ba tare da an dakile su ba yayin da Fulani makiyaya suke ci gaba da mamaye dazuzzukan yankin.
'Yan bindiga sun yi artabu da mutanen gari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mutanen gari sun cire tsoro, sun yi artabu da wasu miyagun 'yan bindiga da suka farmake su a Sokoto.
'Yan ta'addan dauke da makamai sun kai hari ne a wani kauyen Sokoto, inda suka yi awon gaba da mutane masu yawa, suka shiga da su daji.
Sai dai, mutanen kauyen sun yi kukan kura, suka afka cikin dajin tare da fafatawa da miyagun, kuma suka yi nasarar kubutar da wadanda aka sace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


