Hakurin Matasa Ya Fara Karewa, Sun Yi Barazanar Yin Gaba da Gaba da 'Yan Bindiga
- Matasa sun fara fusata kan matsalar tsaro da har yanzu gwamnati ta gaza magance wa a sassan Najeriya
- Matasan yankin karamar hukumar Shagari da ke jihar Sakkwato sun yi wani zama kan hare-hare da cin mutuncin da yan bindiga ke yi a yankinsu
- Sun bukaci gwamnatin jiha da ta tarayya su gaggauta daukar mataki na zahiri ba surutu ba, idan ba haka ba za su dauki makami
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Karuwar hare-hare da garkuwa da mutane a yankin kafamar hukumar Shagari da ke jihar Sakkwato ya fara kai matasa wuya.
Matasan yankin Shagari a Sakkwato sun fara tunanin daukar makamai, su yi gaba da gaba da wadannan yan ta'adda domin kare kansu da yan uwansu.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai fafutukar kare haƙƙin matasa, Bello Bala Shagari, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Gaba ta yi tsanani tsakanin yan bindiga, an kashe wasu jagorori 2 da suka addabi jama'a
Matasan Shagari sun yi zama kan tsaro
Bello Bala Shagari ya bayyana cewa taron yanar gizo da matasan Shagari suka gudanar ya nuna matuƙar damuwarsu kan abin da suka kira gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Sun koka da cewa hare-haren ‘yan bindiga da suka daɗe suna faruwa sun raba iyalai da muhallansu, sun lalata harkokin noma, tare da jefa al’umma cikin tsananin tsoro
Mr. Shagari, wanda jika ne ga tsohon Shugaban Najeriya, Shehu Shagari, ya bayyana cewa matasan sun kai wuya, sun fara tunanin zabin karshe na kare kansu daga hare-hare da cin mutunci.
Matasan Sakkwato sun fara zuwa wuya
A cewarsa, ƙaruwar rashin tsaro ya sanya matasa fara shakku kan karfin gwamnati na aiwatar da kundin tsarin mulki da ya wajabta kare rayukan ‘yan ƙasa.
“Gwamnati ta kasa kare mu. Ba za mu ci gaba da zama a haka muna kallo ana zaluntar jama’armu ba. Kare kai na iya zama zabinmu na ƙarshe.
“Ko da yake matasa na son zaman lafiya, amma ba za mu iya ci gaba da kallo ba yayin da wasu tsageru ke kashe mutane, su na lalata dukiya a kullum,” in ji shi.
Mafitar da matasa suka bai wa gwamnati
Matasan sun yi kira ga gwamnatin jihar Sakkwato da kuma gwamnatin tarayya da su gaggauta tura jami’an tsaro zuwa Shagari da makotan ƙananan hukumomi.
Sun jaddada cewa daukar matakai na gaske shi zai kawo karshen wannan bala'i da ake ciki, ba yawan surutu da daukar alkawurra ba.

Source: Twitter
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun sha gargadi cewa barin jama'a su ɗauki makamai don kare kansu na iya ƙara hura wutar rikici da kuma jinkirta samun zaman lafiya.
Jihar Sakkwato, kamar Zamfara, Katsina da Kebbi, ta shafe shekaru tana fama da matsalar ‘yan bindiga, inda ake yawan yin garkuwa da mutane, kashe-kashe, da kuma kai farmaki ga kauyukan manoma.
Mutane sun yi zanga-zanga kan matsalar tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa daruruwan jama'a 'yan gudun hijira daga kauyuka sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkaato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan rashin tsaro.
Rahoto ya nuna cewa wannan zanga-zanga ta barke ne biyo bayan wani kazamin hari da yan bindiga suka kai kauyen Rinaye a Sakkwato.
An ruwaito vewa maharan sun kashe akalla mutane uku, sannan suka yi awon gaba da hakimai da limaman garin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

