Da Gaske Tinubu Ya ba Dalibar Yobe N200,000? An Gano Wanda Ya Bayar
- An samu ce-ce-ku-ce bayan rahoton da ya nuna daliba Nafisa Abdullahi ta samu N200,000 daga gwamnatin tarayya bayan lashe gasar Turanci
- Ma’aikatar Ilimi ta fitar da wata sanarwa game da kyautar inda ta ce labarin ba gaskiya ba ne duk da karin haske da ta ce an yi
- Ta ƙara da cewa ba a yin kasafin gwamnati don irin wannan kyauta, domin an ware kuɗaɗe ne kawai da nufin bunkasa harkokin ilimi a ƙasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An yi ta maganganu bayan rahoton da ya ce gwamantin tarayya ta ba daliba Nafisa Abdullahi daga jihar Yobe kyautar kudi.
An bayyana cewa an ba Nafisa kyautar N200,000 bayan lashe gasar Turanci da aka yi a London ta kasar Burtaniya tare da wasu daliban.

Kara karanta wannan
Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu

Source: UGC
Martanin ma'aikatar ilimi bayan ba Nafisa N200,000
Ma'aikatar ilimi ta fayyace gaskiya a shafin Facebook domin cirewa mutane shakku kan kyautar da ake cewa gwamnatin tarayya ta ba bayar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatar ta ce abin takaici ne yadda ake ta yada cewa gwamnatin Bola Tinubu ta ba da kyautar N200,000 ga Nafisa.
Sanarwar ta ce labarin da ake yadawa ba gaskiya ba ne saboda kyautar ba daga hannun Bola Tinubu ta fito ba.

Source: Facebook
Wanene ya ba Nafisa kyautar N200,000 a gwamnati?
Ma'aikatar tarayyar ta ce hakan na daga cikin kokarin minista, Tunji Alausa ne domin karawa dalibar watau Nafisa da sauran dalibai karfin guiwa.
Sanarwar ta ce:
"Ma'aikatar ilimi ta ci karo da wani rahoto da ake yadawa kan kudin da aka ba daliban da suka yi nasara a gasar Turanci a London.
"Saboda cire shakku, Ma'aikatar tana mai tabbatar da cewa kyautar da aka ba daliban a ranar 28 ga watan Agustan 2025 kyauta ce daga ministan ilimi, Tunde Alausa.
"Wannan kyauta ba daga gwamnatin tarayya ba ce ko kuma ma'aikatar ilimi da kanta, wanda kuma an sanar a ranar ba da kyautar."
Yadda ma'aikatar ilimi ke kashe kudinta
Ma'aikatar ilimi ta ce ya kamata al'umma su sani babu wani kasafi da aka ware mata domin ba da kyaututtuka ko karrama yan Najeriya.
Ta ce kudin da ake warewa ma'aikatar an tanade su ne domin bunkasa harkokin ilimi kamar yadda tsare-tsaren gwamnati su ke.
Mutane da dama sun nuna rashin jin dadi kan kyautar wanda aka ce gwamnatin tarayya ne ta bayar kafin ma'aikatar ilimi ta yi karin haske.
An ba Nafisa kyautar N200,000 bayan lashe gasa
Kun ji cewa rahotanni sun ce Gwamnatin Tarayya ta gudanar da liyafa ta musamman ga daliba daga jihar Yobe, Nafisa Abdullahi wacce ta lashe gasa ta duniya.
Nafisa tana cikin wadanda suka lashe gasar 'TeenEagle' a London da ke kasar Birtaniya a Nahiyar Turai inda suka yi nasara kan kasashe 20 da suka fafata a gasar.
Tun bayan sanar da nasarar dalibar, an yi ta kiran Bola Tinubu ya karrama ta kamar sauran yan wasan ƙwallon kafa kafin daga baya a ba ta N200,000.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
