Hatsarin Jirgi Ya Yi Muni, Mutane 60 Sun Mutu a Hanyar zuwa Gidan Gaisuwa a Najeriya
- A jiya Laraba, 3 ga watan Satumba, 2025 aka samu labarin kifewar wani jirgin ruwa bayan ya dauko mutane kusan 100 a jihar Neja
- Hatsarin jirgin ya rutsa da mata da yara, wadanda aka gano cewa suna hanyar zuwa ta'aziyyar rasuwa ne a karamar hukumar Borgu
- Shugaban karamar hukumar Borgu ya ce adadin wadanda suka mutu a hatsarin ya karu daga mutane 29, yanzu sun kai akalla mutum 60
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa da ya auku a bakin kogin Malale da ke karamar hukumar Borgu, Jihar Neja, ya karu zuwa mutum 60.
A jiya Laraba aka samu labarin hatsarin jirgin ruwan, wanda bayanai suka nuna ya dauko mutane 90, galibinsu mata da kananan yara.

Source: Getty Images
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa jirgin ruwan ya taso ne daga kauyen Tugan Sule a gundumar Shagunu da ke Borgu, zuwa kauyen Dugga domin ta'aziyyar rasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hatsarin jirgi ya rutsa da masu ta'aziyya
A wata sanarwa da ya fitar, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da cewa an gano gawarwaki 29.
“Mun samu rahoton hatsarin jirgin ruwa a wani gari mai suna Gausawa a yankin Malale. Jirgin ya tashi daga Tugan Sule da mutane 90 ciki har da mata da yara, za su kauyen Dugga domin gaisuwar rasuwa.
"Lamarin ya faru ranar Talata, 2 ga Satumba 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe, kuma musabbabin hatsarin sune lodi fiye da ƙima da kuma karo da kututturen bishiya a cikin ruwa,” in ji shi.
Mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin sun kai 60
Sai dai a rahoton Reuters, shugaban karamar hukumar Borgu, Hon. Yarima Kilishi Sulayman ya bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu ya karu sosai.
“Yawan mutanen da suka mutu ya haura zuwa 60. An gano mutane 10 cikin mummunan yanayi yayin da har yanzu ana ci gaba da neman wasu,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Hatsarin jirgi ya rutsa da mutane kusan 100 a hanyar zuwa gidan gaisuwa, an rasa rayuka

Source: Facebook
Yadda ake aikin ceto fasinjoji a ruwa
Hakazalika, mai unguwar Shagumi, Sa’adu Inuwa Muhammad, ya tabbatar da cewa ya isa wurin bayan faruwar hatsarin.
"Na je wurin jiya daga ƙarfe 12:00 na rana har zuwa 4 na yamma. Jirgin ya ɗauko mutane sama da 100. Mun gano gawarwaki 31 daga kogin, sannan an ciro jirgin daga ruwa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an binne mutane hudu a ranar Talata bisa tsarin addinin Musulunci, kuma mafi yawansu mata da yara ne.
Manoma sun mutu a hatsarin jirgi a Borno
A wani rahoton, kun ji cewa an rasa rayuka yayin da jirgin ruwa da ya dauko manoma akalla 20 ya gamu da hatsari a jihar Borno ranar Litinin.
Wani mazaunin yankin, Audu Abu, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike don gano ko akwai wasu da suka bace.
A rahoton da hukumar ba da agajin gaggawa watau NEMA ta fitar kan abin da ya faru, ta ce an yi nasarar ceto mutane 17 a raye yayin da sauran mutum uku suka rasu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
