Abinci: Kano, Gombe, Jihohin Arewa 11 Sun Samu Tallafin Amurka na ₦49.686bn
- An samar da tallafin abinci mai gina jiki ga dubban mutanen da rikice-rikice suka raba da muhallansu a wasu yankunan Najeriya
- Tallafin da gwamnatin kasar Amurka ta bayar zai taimaka wajen kai agaji ga mutane sama da 764,000 a jihohin Arewa 13
- Mata masu juna biyu da masu shayarwa da kuma yara kanana za su amfana da tallafi na musamman a yankunan da aka ambata
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin Dala miliyan 32.5 (₦49.686bn) ga shirin Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) domin kai agaji Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa an yi tanadin ne domin samar da agajin abinci mai gina jiki ga mutanen da rikice-rikice suka raba da muhallansu a Najeriya.

Source: Getty Images
Ofishin jakadancin Amurka ya wallafa cewa tallafin zai baiwa WFP damar kai agaji ga mutane 764,205 da ke fuskantar matsanancin hali a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa yankunan biyu sun fi fama da matsalar rashin tsaro da ƙaurace-ƙaurace.
Amfanin tallafin Amurka a Najeriya
A sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya fitar, an bayyana cewa gudummawar na da nufin tallafawa masu rauni da kuma taimakawa wajen rage matsalar yunwa da ƙarancin abinci.
Rahoton ya bayyana cewa za a rarraba abinci na yau da kullum ga wasu rukuni na jama’a masu bukata.
A cikinsu har da mata masu juna biyu da masu shayarwa 41,569 da kuma yara 43,235 da za su karɓi abinci mai gina jiki.
An kuma bayyana cewa wannan tsari zai taimaka wajen tallafawa iyalai da dama waɗanda suka rasa komai sakamakon hare-hare da tashe-tashen hankula, musamman a ƙauyuka.
Matsalar tsaro da yunwa a Arewacin Najeriya
A Arewa maso Gabas, jama’a sun sha fama da tashe-tashen hankulan Boko Haram da ya haifar da ƙaurace-ƙaurace da lalata ƙauyuka.
Saboda tashin hankalin, al’ummomi da dama sun rasa gonaki da hanyoyin samun abinci a jihohi 6 na yankin, musamman Borno da Yobe.
A Arewa maso Yamma kuwa, matsalar ta bambanta, domin ‘yan bindiga da hare-haren fashi sun haifar da barace-barace da ƙaruwar rashin tsaro, lamarin da ya kara tsananta matsalar yunwa.
Wannan ya sanya dubban mutane cikin halin dogaro da tallafin abinci daga ƙasashen waje da kungiyoyin agaji.

Source: Facebook
Jihohin Arewa ta Yamma da za su samu tallafin su ne:
1. Jigawa
2. Kaduna
3. Kano
4. Katsina
5. Kebbi
6. Sokoto
7. Zamfara
Jihohin Arewa maso Gabas kuma su ne:
1. Adamawa
2. Bauchi
3. Borno
4. Gombe
5. Taraba
6. Yobe
Taimakon da aka samu daga Amurka
Tun daga shekarar 2019, gwamnatin Amurka ta ce ta tallafa wa manoma sama da miliyan 5 a Najeriya ta hanyar shirye-shiryen USAID.
Punch ta wallafa cewa Amurka ta ce shirye shiryen sun taimaka wajen ƙarfafa noman gargajiya da kuma bunkasa tattalin arzikin ƙauyuka.
A Disamban 2024, USAID ta nesanta kanta daga wani rahoto da ya zargi Amurka da rashin gaskiya, inda ta tabbatar cewa dukkan shirye-shiryenta na gudana cikin tsari da bin doka.
Legit ta tattauna da Ahmad Murtala
Wani matashi a jihar Gombe, Ahmad Murtala ya ce ba abin farin ciki ba ne domin Amurka ta kawo tallafin abinci a Najeriya.
Ahmad ya ce:
"Ba abin farin ciki ba ne a ce an kawo tallafin abincin da aka noma Najeriya daga Amurka, me ya sa ake korar manoma a gonakinsu a Najeriya?"
"Noma ya kamata mu yi tunda muna da kasar noma."
Nnamdi Kanu ya nemi agajin Amurka da Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban 'yan kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya rubutawa shugabannin duniya wasika.
A cikin wasikar, Kanu ya roki shugaba Donald Trump da sauran masu fada a ji na duniya su saka baki a sake shi.
Tun a lokacin mulkin marigayi shugaba Muhammadu Buhari aka kama Kanu a kasar Kenya aka taso keyar shi zuwa Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


