Bayan Rasuwarsa, Tinubu Ya Fadi Yanayin Kasar da Buhari Ya Damka Masa

Bayan Rasuwarsa, Tinubu Ya Fadi Yanayin Kasar da Buhari Ya Damka Masa

  • Shugaba Bola Tinubu ya sake tuna tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, inda ya yi masa addu'o'i na musamman
  • Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kafa ’yan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaro da suka addabi ƙasa
  • Shugaban ya kuma umurci sojoji da su tura kayan zamani da na’urorin sa ido a Katsina domin dakile hare-haren ’yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake tunawa da marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ganin ayyukan alheri da ya yi tare da yi masa addu'o'i.

Tinubu ya yi wa gwamna Radda alkawari kan tsaro
Shugaba Bola Tinubu da gwamna Radda na Katsina da ke fama da rashin tsaro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Dikko Umaru Radda.
Source: Twitter

Tinubu ya magantu kan 'yan sandan jihohi

Tinubu ya bayyana haka ne bayan karbar bakuncin wasu fitattun 'yan Najeriya karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

An yi ganawar a fadar shugaban kasa a ranar Laraba 3 ga watan Satumbar 2025 inda suka tattauna muhimman batutuwa.

Yayin ganawar, Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙirƙiri ’yan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaro.

Ya ce hakan ya zama dole domin tabbatar da shi yadda ya kamata a fadin ƙasar nan duba da yadda matsalolin tsaro suka yi katutu, Vanguard ta ruwaito.

Tinubu ya kuma umurci rundunar sojoji da su tura kayan yaƙi na zamani tare da na’urorin sa ido a Katsina domin dakile hare-haren ’yan bindiga kan fararen hula.

Buhari ya sake addu'o'i ga Buhari bayan rasuwarsa
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Bola Tinubu. Hoto: Bashri Ahmad, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Tinubu ya sake tuna alherin Buhari a Najeriya

Kan jimamin mutuwar Muhammadu Buhari, Tinubu ya tabbatar da cewa za a karrama shi, domin a tuna gagarumin gudunmawa da ya bayar.

Ya ce:

“Lokacin da muka rasa ɗan’uwanmu, Buhari, rashi ne ga kowa da kowa, wannan nufin Allah Maɗaukakin Sarki ne.
"Amma ya nuna kyawawan halaye, bai mika mani lalatacciyar ƙasa da ta sha wahala a tsarin siyasa da ya rushe ba.

Kara karanta wannan

Farashin Dala: Bincike ya karyata ikirarin Tinubu kan farfado da darajar Naira

"Sai dai ya bar mani kasa mai cike da nasara, wanda shi ne mafi muhimmanci."

Tinubu ya ba da tabbacin cewa za su mika komai ga Ubangiji bayan rasuwar Buhari tare da yi masa addu'ar samun gidan aljanna.

Ya ce a yanzu ba lokaci ne na tuna abubuwan da suka faru a baya ba na bakin ciki sai dai a tunkari gaba domin samun nasara a Najeriya.

Ya kara da cewa:

“Dole mu ci gaba da yin addu’a cewa Allah Maɗaukaki ya saka shi a Aljannah Firdausi, ya kuma ba mu sauran ƙarfi mu tsaya da ƙarfi mu tura Najeriya gaba.
"Ba za mu ci gaba da waiwayen baya cikin bakin ciki ba, sai dai mu ci gaba cikin nasara.”

Obasanjo ya soki gwamnatocin Buhari da Tinubu

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya sake caccakar gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa gwamnatin farar hula ta Buhari, ita ce mafi muni da aka taba yi a tarihin Najeriya.

Hakazalika, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kamo hanyar gazawa kamar wacce ta gabace ta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.