Lokaci Ya Yi: Yanayin da Wani Likita Ya Rasu a Asibiti Ya Ja Hankali, NARD Ta Yi Magana

Lokaci Ya Yi: Yanayin da Wani Likita Ya Rasu a Asibiti Ya Ja Hankali, NARD Ta Yi Magana

  • Kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta koka kan yadda ake cika wa mambobinta aiki a asibitoci a Najeriya
  • Hakan na zuwa ne bayan wani lokita ya mutu sakamakon gajiya daga aikin da ya yi na kwanaki uku a jere ba tare da hutawa ba a RSUTH
  • Wannan lamari bai yiwa kungiyar NARD dadi ba, inda ta fito ta sake kira ga gwamnati kan ayyukan da ake dora wa likitoci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Oluwafemi Rotifa, wani matashin likita mai neman kwarewa da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Rivers (RSUTH), ya riga mu gidan gaskiya.

Likitan ya rasa ransa ne bayan shafe tsawon awanni 72 yana aikin duba marasa lafiya ba tare da hutawa ba a asibitin RSUTH.

Dr. Oluwafemi Rotifa.
Hoton likitan da ya rasu bayan shafe kwanaki 3 yana aiki a jere a asibitin RSUTH Hoto: Adimorah Aneke
Source: Facebook

Rahotan The Cable ya bayyana cewa Dr. Rotifa ya fadi ya mutu ne a ranar Litinin bayan ya shiga ɗakin hutawa don yin barci.

Kara karanta wannan

Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda likita ya rasu bayan aikin kwana 3

Duk da ƙoƙarin da aka yi na ceto rayuwarsa a sashen kula da marasa lafiya na musamman (ICU), bai cimma nasara ba, daga bisani aka tabbatar da ya rasu.

An ce ya shafe kwana uku a jere yana aikin ujila a asibitin ba tare da hutawa ba, lamarin da ake zargin shi ne ya zama ajalinsa.

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban ƙungiyar likitocin masu neman kwarewa ta Najeriya (NARD), Tope Osundara, ya soki yadda ake ɗora wa likitoci nauyin aiki fiye da ƙima a asibitocin ƙasar nan.

Kungiyar NARD ta koka kan aikin likitoci

“Wahalar aiki da gajiyar da likitoci ke fuskanta na ƙara zama abin damuwa sosai. Mun koka kan wannan lamari kuma mun mika korafi a hukumance amma har yanzu shiru," in ji shi.

Ya bayyana cewa an yi wa marigayi Rotifa kiran gaggawa a dakin kula da marasa lafiya, inda bayan ya duba wani mara lafiya, sai ya koma ɗakin hutawa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya

Shugaban NARD ya ci gaba da cewa an samu Rotifa a kwance a ƙasa, inda ake kyautata zaton cewa ya fado ne daga gado.

NARD ta aika sako ga gwamnatin Najeriya

Dr. Osundara ya ce wasu likitoci kan shafe wata ɗaya gaba ɗaya suna aiki babu hutu.

“A gaskiya, bai kamata mutum ya yi aikin fiye da awa 24 ba. Mun gano cewa yana fama da zazzabin cizon sauro, amma duk da haka sai ya ci gaba da kula da marasa lafiya.
"Yawan aiki da ya yi ya sa ya rasa karfin jikinsa kuma ya haifar da wannan mutuwa mai raɗaɗi,” in ji shi.
Asibitin koyarwa na jami'ar jihar Ribas.
Hoton babbar kofar shiga asibitin koyarwa na jami'ar jihar Ribas (RSUTH) Hoto: GetFreee Sence Medium
Source: Facebook

Shugaban NARD ya bukaci gwamnati ta magance ƙarancin ma’aikata, ta inganta jin daɗin likitoci tare da sanya tsarin aiki mai sauƙi da ya dace da lafiyar ɗan adam.

Tsohon shugaban jami'ar Edo, Dawood ya mutu

A baya, mun kawo maku cewa tsohon mukaddashin shugaban jami’ar jihar Edo da ke Iyahmo, Farfesa Dawood Egbefo, ya kwanta dama.

An ruwaito cewa Farfesa Dawood ya rasu ne bayan kimanin makonni biyu da Gwamnan Edo ya nada sabon shugaba a jami'ar jihar.

Rasuwarsa ta girgiza jami’ar, inda malamai da dalibai ke bayyana shi a matsayin mutum mai jajircewa kuma dattijo mai hangen nesa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262