Ministan Buhari Ya Karyata Zargin Kashe N100bn don Samar da Jirgin Saman Najeriya
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce aikin 'Nigeria Air' da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ƙirƙira ba yaudara ba ne
- Sirika ya kuma yi karin haske a kan zargin cewa an kashe N100bn a aikin da wasu ke ganin an yi rufa rufa tare da handame kudin kasa
- Hukumar EFCC na tuhumarsa da karkatar da kwangiloli ga kamfanonin iyalansa, amma ya ce batun yana kotu, saboda haka ba zai yi sharhi ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya bayyana cewa aikin 'Nigeria Air' da gwamnatin Muhammadu Buhari ta tsara babu yaudara a cikinsa.
Ya bayyana haka ne a lokacin da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ke tuhumarsa kan karkatar da kwangiloli da wasu badakaloli a kan batun.

Kara karanta wannan
Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu

Source: Facebook
A hirarsa da Channels Television, ya ce gwamnati ta bi dukkannin matakan doka wajen aiwatar da aikin tare da samun sahalewar Hukumar ICRC.
Ministan Buhari ya musanta zargin almundahana
Jaridar The Punch ta wallafa cewa Sirika ya musanta batun kashe N100bn a wajen gudanar da aikin da ya dauki hankulan 'yan kasa.
Ya ce jimillar kuɗin da aka ware wa aikin jirgin N5bn ne, kuma daga ciki an fitar da N3bn kacal, wanda ya saba da abin da ake yada wa.

Source: Facebook
Hadi Sirika ya kara da bayyana cewa an fi karkatar da kuɗin wajen biyan masu ba da shawara da albashin ma’aikata.
Ya ce:
“Tasirin shari’ar da wasu kamfanonin jirgin sama suka shigar a kotu ne ya tsayar da aikin, ba wai rashin bin tsari ba."
Ya ce kamfanonin Airspeace, United da Azman ne suka shigar da ƙara suna kalubalantar matsayin gwamnati wajen mallakar 5% a sabon jirgin.

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci
Ana shari'a da Ministan Buhari
Bayan barin ofis a 2023, Sirika ya fuskanci shari’o’i kan zargin almundahana da cin hanci da hukumar EFCC ke yi masa.
EFCC ta zarge shi da baiwa kamfanonin iyalansa kwangiloli masu darajar biliyoyin Naira, ciki har da na diyarsa Fatima Sirika da surukinsa Jalal Hamma.
Da aka tambaye shi ko ziyararsa fadar shugaban ƙasa ta shafi neman sassauci kan shari’arsa, Sirika ya ce batun yana gaban kotu kuma bai dace a yi masa tsokaci a kafafen yada labarai ba.
Ya ce:
“Dalilin zuwa fadar shugaban ƙasa shi ne gaisuwa da jaje ga shugaban ƙasa saboda rasuwar shugaba Buhari, sannan mu gode masa bisa irin gudummawar da yake bayarwa."
Tsohon Minista ya fadi matsayarsa kan ADC
A baya, mun wallafa cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika, ya bayyana matsayarsa kan rade-radin da ke cewa yana cikin hadakar ‘yan adawa.
Tsohon Ministan da hukumar EFCC ke shari'a da shi ya nesanta kansa daga wannan batu, yana mai cewa rahotannin da ke yawo ba su da tushe ballantana makama.
Hadi Sirika ya tabbatar da cewa ya ziyarci fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Talata, inda ya gana da Cif Bayo Onanuga, amma ba a kan shari'arsa da hukumar yaki da cin hanci ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng