Farashin Dala: Bincike Ya Karyata Ikirarin Tinubu kan Farfado da Darajar Naira
- Shugaba Bola Tinubu ya yi ikirarin cewa ya samu Dalar Amurka tana kan N1,900 a lokacin hawansa mulki a 2023, ya ce yanzu ta dawo N1,450
- A shekarar 2023 ne shugaba Bola Tinubu ya hau mulkin Najeriya bayan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa'adi biyu
- Legit Hausa ta yi bincike domin tabbatar wa ko akasin haka kan ikirarin da shugaba Tinubu game da farashin Dala bayan shekara biyu a kan karaga
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – A jawabin da ya gabatar ranar Laraba, 3 ga Satumba 2025, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce lokacin da ya hau mulki a 29 ga Mayu 2023, Dala tana daidai da N1,900.
Yayin da ya ke jawabin, shugaban kasar ya nuna cewa matakan da ya dauka sun nuna cewa Dalar Amurka ta dawo daidai da N1,450.

Kara karanta wannan
Jibrin Kofa: Na kusa da Kwankwaso ya fadi matsalar Arewa a shirin kifar da Tinubu a 2027

Source: Facebook
Imrana Muhammad ya wallafa bidiyon bayanin da shugaban kasar ya yi da yadda ya yi ikirarin cewa Naira ta farfado sosai a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai bincike ya nuna cewa wannan ikirari ba shi da tushe, domin a lokacin hawansa, Naira ba ta kai wannan mummunan matsayi ba.
Darajar Dala da Naira kafin zuwan Tinubu
Tribune ta wallafa cewa kafin 29 ga Mayu 2023, Najeriya tana amfani da tsarin musayar kudi fiye da ɗaya.
Babban bankin ƙasa, CBN, yana sauya Dala 1 zuwa Naira tsakanin N460 zuwa N470 kuma wannan shi ne tsarin da yawancin harkokin kasuwancin gwamnati ke bi.
A gefe guda kuma, kasuwar bayan fage wacce ta shafi jama’a kai tsaye ta na musanya Dala a kusan N750 a lokacin.

Source: Facebook
Dala 1 ta dawo N1,900 a mulkin Tinubu
Bincike ya nuna farashin Dala bai kasance N1,900 a watan Mayu 2023 ba, kamar yadda Tinubu ya fada.
A zahiri, wannan ya faru ne bayan gwamnatinsa da CBN sun aiwatar da wasu manyan sauye-sauye na tattalin arziki.
A ranar 29 ga Mayu 2023 an cire tallafin man fetur, sannan a ranar 14 ga Yuni 2023, CBN yi sauye sauye game da tattalin arziki.
Wannan ya sa darajar Naira ta ragu sosai, inda a watan Fabrairu da Maris 2024 darajar Naira ta shiga matsayi mafi rauni – Dala ta kusan N1,800 zuwa N1,900 a kasuwar bayan fage.
Darajar Naira a Agustan 2025
A jawabin sa, TVC ta rahoto shugaban ya ce Dala ta koma N1,450 a watan Agusta 2025 sai dai bincike ya nuna wannan ma ba daidai ba ne.
A ranar 29 ga Agusta 2025, rahotannin kasuwa sun nuna Dala tana da darajar N1,525 a kasuwar bayan fage, yayin da CBN ta ke canja ta a N1,531.45 a hukumance.
Sakamakon binciken ikirarin Tinubu
Da wannan, bincike ya tabbatar da cewa ikirarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cewa ya samu Dala a kan N1,900 a ranar hawansa mulki a 2023 ba gaskiya ba ne.
Haka zalika, cewa Naira ta koma N1,450 a watan Agusta 2025 ba daidai ba ne, domin bayanai sun tabbatar da cewa ta tsaya a kusan N1,525 a kasuwar bayan fage da kuma N1,531.45 a CBN.
A taƙaice: Tinubu ya yi amfani da bayanan da ba su dace da tarihi ba wajen bayyana nasarorin gwamnatinsa a fagen tattalin arziki.
Tinubu ya ce tattalin arziki ya farfado
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce tattalin arzikin kasar ya farfado.
A kan haka ne Bola Tinubu ya ce kasar ba ta cikin fargaba kan harajin da shugaban Amurka ya lafta wa kasashe.
A farkon watan Agustan 2025 ne shugaba Trump ya rattaba hannu kan dokar lafta wa kasashe duniya haraji ciki har da Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

