Gwamnonin Arewa Sun Gana da Tinubu a Abuja, Sun Roƙi Manyan Alfarma 2
- Gwamnonin Arewa maso gabashin Najeriya sun yi wata ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Abuja
- Gwamnonin yankin sun tura bukatu na musamman ga shugaban Najeriyan domin kawo sauyi da ci gaba a jihohinsu
- Babagana Zulum shi ya jagoranci gwamnonin Arewa maso Gabas wajen ganawar inda suka bukaci kammala manyan ayyukan hanyoyi 17
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya jagoranci tawagar gwamnonin Arewa domin ganawa da Bola Tinubu.
Zulum ya jagoranci gwamnonin ne daga Arewa maso Gabas domin tura bukatunsu ga shugaban a yau Laraba a Abuja.

Source: Facebook
Bukatun gwamnonin Arewa maso gabas ga Tinubu
Daraktan yada labaran gwamna Inuwa Yahaya na Gombe, Isma'ila Uba Misilli ya tabbatar da haka a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da taron ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda aka tattauna batutuwan masu muhimmanci.
Daga cikin batutuwan akwai kammala hanyoyi 17 masu muhimmanci a yankin domin kawo ci gaba.
Haka kuma, an bukaci a ci gaba da aikin hako mai a rijiyoyin Kolmani da na Tafkin Chadi domin bunkasa tattalin arzikin yankin.
Gwamnonin da suka yi zama da Tinubu
Gwamnonin da suka halarta sun hada da Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe, Bala Muhammad na Bauchi, Mai Mala Buni na Yobe.
Sauran sun hada da Agbu Keffas na Taraba da Ahmadu Umaru Fintiri daga jihar Adamawa wadanda gaba daya suka mara wa Zulum baya a matsayin shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas.

Source: Facebook
Hanyoyin da ake neman Tinubu ya gyara
A jawabinsa, Zulum ya roki shugaban kasa ya kammala manyan ayyukan hanyoyi da gina sababbin hanyoyin da ke hade jihohin yankin gaba daya.
Hanyoyin sun hada da Kano-Maiduguri, Port Harcourt-Jos-Bauchi-Maiduguri, Bama-Mubi-Yola, Wukari-Jalingo-Yola, Duguri-Mansur da kuma Bauchi-Gombe-Biu-Damaturu.
Sauran sun hada da Damaturu-Geidam, Bauchi-Ningi-Nasaru-Babaldo, Gombe-Potiskum, Damaturu-Biu, Alkaleri-Futuk, Maiduguri-Damboa-Yola da kuma Gombe-Dukku-Darazo.
Bugu da kari akwai Biu-Gombe, Ibi-Shamdam, Maiduguri-Monguno-Baga da kuma Maiduguri-Ngala-Bama-Banki, wadanda ake ganin suna da matukar muhimmanci.
Alkawuran gwamnonin ga Bola Tinubu
Zulum ya gode wa shugaban kasa kan jajircewar dawo da zaman lafiya a yankin inda ya jaddada masa goyon bayansu.
Zulum ya ce:
“Mai girma shugaban kasa, gwamnonin Arewa maso Gabas muna ba ka daraja ta musamman kuma dukanmu mun yanke shawarar kasancewa tare da kai."
Shugaba Tinubu a martaninsa ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin bunkasa yankin Arewa maso Gabas.
Gwamnonin Arewa sun yi kira ga Tinubu
A baya, mun ba ku labarin cewa gwamnonin yankin Arewa maso Gabas sun fito sun yi gargadi na musamman game da abin da zai faru a Najeriya a 2026.
Gwamnonin sun bayyana cewa za a samu tsadar kayan noma da zai iya haddasa ƙarancin abinci a shekarar 2026 da ke tafe.
Sun roƙi gwamnati ta kara tallafin manoma da kuma fadada shirin noma na damina da rani domin kauce wa matsalolin abinci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

