Faransa Ta Dawo da Ƙoƙon Kawunan Sarakuna a Afrika bayan Kashe Su
- Faransa ta cika alkawarin da ta dauka ga Madagascar bayan shafe shekaru da dama game da kisan wasu sarakuna
- Ƙasar ta cika alkawarin ne bayan dawo da kokon kawunan sarakuna uku bayan shekaru 128 da aka kashe su
- Faransa ta mika su bisa sabuwar dokar 2023 wacce ta sauƙaƙa dawo da kayan tarihi a taron ban girma a Antananarivo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Antananarivo, Madagascar - Jami'an gwamnatin kasar Madagascar sun gana da wasu wakilan kasar Faransa a wani gagarumin taro.
A ranar Talata, Madagascar ta gudanar da wani babban biki na dawo da kokon kawunan sarakuna uku da aka kwashe shekaru 128 da suka gabata.

Source: Getty Images
Madagascar ta karbi kokon kawuna sarakuna daga Faransa
Ana kyautata zaton daya daga cikinsu kawun Sarki Toera ne na kabilar Sakalava, wanda aka kashe lokacin mamayar mulkin mallaka, cewar Al Jazeera.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa, kawunan da suka hada da na Sarki da jarumansa biyu, sojojin Faransa ne suka kwace su a 1897, suka tafi da su Paris.
A can aka ajiye su a gidan kayan tarihi a matsayin kayan ganima na yaki, kamar yadda miliyoyi suka tabbatar.
An mika kokon kawunan ga hukumomi wanda kasar Faransa ta yi bisa sabuwar dokar 2023 wacce ta ba da damar dawo da gawarwaki da aka kwace a lokacin mulkin mallaka.
Sun iso Antananarivo ranar Litinin da dare, inda wakilan Sakalava cikin kayan gargajiya suka tarbe su a filin jirgi da girmamawa, France 24 ta ruwaito.

Source: UGC
An kai kokon kawuna makabarta domin birne su
A ranar Talata kuma, an dauke su cikin kwalaye da aka lullube da tutar Madagascar, aka yi jerin gwanon mota a babban birnin har zuwa makabarta.
Shugaba Andry Rajoelina, jami’an gwamnati da kuma dattawan kabilar Sakalava sun halarci wannan bikin tarihi na dawo da kawunan kakanninsu.
Za a tafi da kawunan zuwa Belo Tsiribihina, wani gari da ke gabar yammacin teku, kilomita 320 daga Antananarivo, domin birne su.
A lokacin mika su a Paris, Ministan Al’adu na Faransa, Rachida Dati, ta bayyana cewa kwamitin bincike ya tabbatar da cewa kawunan na Sakalava ne.
Amma sun ce za a iya kyautata zaton cewa daya daga cikin kawunan da aka kawo na Sarki Toera ne.
Shin akwai sauran kokon kawunan sarakuna a Faransa?
Wannan mataki wani bangare ne na sabon nazari da Faransa ke yi game da tarihin mulkin mallakanta.
Kafin wannan lokaci, sai majalisa ta amince kafin a dawo da irin wadannan abubuwa.
Madagascar, wacce ta sha mulkin mallakar Faransa sama da shekaru sittin kafin samun ’yancin kai a 1960, har yanzu tana da daruruwan kawunan kakanninta a Faransa.
Faransa ta horas da jami'an NDLEA a Najeriya
Kun ji cewa gwamnatin Faransa ta tabbatar wa NDLEA tallafin horaswa, karin kwarewa da kayan aiki domin yakar ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Laftanal Janar Regis Colcombet ya ce tattaunawar na daga cikin yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin shugaba Emmanuel Macron da Bola Tinubu.
Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (Mai ritaya) ya bukaci karin horo kan dabarun aiki, binciken intanet da kuma fasahar zamani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

